Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutane 14 a Wani Gari a Kaduna
- Yan bindiga sun yi awon gaba da akalla mutane 14 a Unguwar Iri Station a karamar hukumar Kajuru a Kaduna
- Bala Jonathan, wani kansila na mulki da kuɗi da lafiya a yankin ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa da safe suka kai harin
- Rundunar yan sanda Jihar Kaduna ba ta tabbatar da afkuwar lamarin ba amma ta yi alƙawarin za ta bincika sannan ta yi ƙarin bayani
Kaduna - Wasu yan bindiga a safiyar ranar Asabar sun kai hari Unguwar Iri Station, Idon Ward a karamar hukumar Kajuru sun sace a ƙalla mutane 14.
Wani kansila na mulki, kudi da lafiya, Bala Jonathan, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce sun kai harin ne a asubahi na ranar Asabar, rahoton The Punch.
Da Duminsa: Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Kwana Kadan Zaben Fidda Gwani Na Yan Takarar Shugaban Kasa a APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jonathan ya bada sunan wadanda aka sace kamar haka: Abdullahi, Yakubu Isah, Samson Julius, Pasema Daniel, Angelina Julius, Junior, Bobo Julius, Saratu Mohammed, Asanath Sunday, Confidence Jerry, Barnaki Sunday, Moses Kenneth, Danladi Goma da Ummi Jibrin.
"Wadannan sune sunayen wadanda aka sace a Iri Station da muka gano a zuwa yanzu. Abin bakin cikin ya faru ne a safiyar yau, 4 g watan Yunin 2022," in ji shi.
Ya kara da cewa an sace wasu yan garin tunda farko "kuma har yanzu suna tsare domin yan uwansu da mutanen garin sun gaza tara kudin da masu garkuwar ke nema."
An gano cewa miyagu sun fara addabar garin na Idon suna sace mutane kuma yan uwansu dole su nemo kudin da za su fanso su.
Gwamnatin Jihar Kaduna bata riga ta tabbatar da afkuwar lamarin ba a lokacin wallafa wannan rahoton.
Da aka tuntuɓe shi a wayar tarho, kakakin yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya yi alkawarin zai tuntubi jami'in da ke kula da yankin sannan ya bawa wakilin The Punch bayani amma ba a ji daga gare shi ba har zuwa lokacin hada rahoton.
"Bari in kira kwamandan yankin sannan in sake tuntubar ka," Jalige ya shaida wa wakilin The Punch.
Dakarun MNJTF Sun Kashe 'Yan Boko Haram Da ISWAP 805 Da 'Yan Bindiga 5 a Benue
A wani rahoton, Dakarun hadin gwiwa na kasashe masu yaki da Boko Haram, MNJTF, sun kashe yan Boko Haram/ISWAP guda 805 yayin wani atisaye na kawar da yan ta'addan da aka fara a watan Maris din wannan shekarar.
Ta ce ta bullo da sabbin dabaru na yaki da ta'addanci hakan yasa ta samu wannan nasarorin cikin wannan lokacin, rahoton The Punch.
2023: 'Yan Kudu Surutu Kawai Suka Iya, Arewa Za Ta Fitar Da Shugaban Ƙasa, In Ji Babban Fasto a Najeriya
Kwamandan MNJTF, Manjo Janar Abdul-Khalifa Ibrahim, ya ce atisayen ya kunshi sojojin kasa, na ruwa da sojojin sama a kokarinsu na fatattakar yan ta'addan ISWAP/Boko Haram da ke buya a yankin Tafkin Chadi.
Asali: Legit.ng