2023: 'Yan Kudu Surutu Kawai Suka Iya, Arewa Za Ta Fitar Da Shugaban Ƙasa, In Ji Babban Fasto a Najeriya

2023: 'Yan Kudu Surutu Kawai Suka Iya, Arewa Za Ta Fitar Da Shugaban Ƙasa, In Ji Babban Fasto a Najeriya

  • Gabanin babban zaben 2023, Apostle Johnson Suleman ya ce Arewa ne za ta sake fitar da shugaban kasa bayan wa'adin Shugaba Buhari
  • Fitaccen malamin addinin kiristan ya ce yan arewa suna da hadin kai wurin cimma bukatarsu ta siyasa amma yan kudu surutu kawai suka iya
  • Suleman ya bada misali da janye takara da Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan Jihar Sokoto ya yi wa Atiku Abubakar a zaben fidda gwani na shugaban kasa a PDP a matsayin hadin kan yan arewa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban cocin Omega Fire Ministries, Apostle Johnson Suleiman, yana tantamar cewa kudu za ta iya fitar da shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023, rahoton The Punch.

Ya bayyana hakan ne yayin wa'azi da ya yi a cocinsa a Abuja, yana mai cewa yan arewa suna da hadin kai kuma suna aiki tare.

Kara karanta wannan

2023: Allah ne ya turo Tinubu ya gyara Najeriya, inji fitaccen malamin addini

2023: 'Yan Kudu Surutu Kawai Suka Iya, Arewa Za Ta Fitar Da Shugaban Ƙasa, In Ji Babban Fasto a Najeriya
2023: Kudu Surutu Kawai Suka Iya, Arewa Za Ta Fitar Da Shugaban Ƙasa, Apostle Suleiman. Hoto: Apostle Johnson Suleiman.
Asali: Facebook

Ya bada misali da yadda Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya janye takararsa ya goyi bayan wani dan arewan, Atiku Abubakar wurin zaben fidda gwani na APC a Abuja a ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya samu kuri'u 371 inda ya doke mai biye da shi, Nyesome Wike wanda ya samu kuri'u 237, sai tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki wanda ya zo na uku da kuri'u 70.

Suleiman ya ce:

"Kun ga abinda ya faru a jiya a Abuja? Me yasa kuke tunanin yan arewa ke mulki tsawon shekaru? Ko da ba dan arewa bane shugaban kasa, arewa ce ke mulki.
"Idan kuma ba su ne ke juya kasar ba, na su ne shugaban kasa. Hakan na faruwa ne domin yan kudu surutu kawai suka iya. Arewa za ta kyalle ka ka gama surutunka zai su baka mamaki. Atiku ya san yan kudu surutu kawai suka iya, kuma ya yi aiki a hakan.

Kara karanta wannan

An Rotsa Wa Wani Kai Da Kwalban Giya a Mashaya Ya Mutu a Bayelsa

"Suna tare da juna dari bisa dari; Hakan yasa Tambuwal ya dauki wannan matakin. Abokanai na na arewa ba su zagi na, amma yan kudu ne suke cin mutunci na."

Buratai: Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasan Najeriya Ya Ba Wa APC Gudunmawar Motar Kamfen Ƙirar Najeriya

A wani rahoton, tsohon babban hafsan sojin kasa kuma Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Janar Tukur Buratai; Babban Kwamishinan Najeriya a Jamhuriyar Zambia, Nwanebike Oghi da kuma wasu jakadu na musamman a ranar Laraba sun bai wa shugabancin jam’iyyar APC kyautar motoci kirar bas mai daukar mutum 18.

Farar motar, wacce kamfanin Innoson Motors ne ya kerata sabuwa ce kuma a jikinta a rubuta “Jakadu na musamman ne su ka bayar da kyautarta,” The Punch ta ruwaito.

Sun gabatar da motar ne a babban ofishin jam’iyyar da ke Abuja bayan wakilan sun yi taron sirri da shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu.

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC su na tunanin mikawa Buhari sunayen mutum 2, sai ya zabi Magajinsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel