Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Kwana Kadan Zaben Fidda Gwani Na Yan Takarar Shugaban Kasa a APC

Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Kwana Kadan Zaben Fidda Gwani Na Yan Takarar Shugaban Kasa a APC

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabon direka janar da zai jagoranci Cibiyar Habbaka Ayyuka, PRODA, da ke Enugu
  • An nada Dr Peter Ogboge a ranar Juma'a, 3 ga watan Yuni, cikin wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban fadar ma'aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari
  • Ogboge ya samu lambobin yabo da dama ya kuma rike mukamai masu yawa a baya kuma ya rubuta kasidu da dama

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A ranar Juma'a 3 ga watan Yuni, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Peter Ogboge a matsayin direka janar da zai jagoranci Cibiyar Habbaka Ayyuka, PRODA, da ke Enugu.

Sabon nadin da shugaban kasar ya yi, Daily Trust ta rahoto yana cikin wani wasika ne mai dauke da sa hannun shugaban fadar ma'aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari.

Kara karanta wannan

Ahmed Idris: EFCC Ta Sako Dakataccen Akanta Janar Da Ake Zargi Da Wawure N170bn

Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Kwana Kadan Zaben Fidda Gwani Na Yan Takarar Shugaban Kasa a APC
Buhari Ya Yi Sabon Nadi Ana Kwana Kadan Zaben Fidda Gwani Na Yan Takarar Shugaban Kasa a APC. Hoto:Fadar Shugaban Kasar Najeriya.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasikar mai kwanan wata na ranar 20 ga watan Mayu, ta ce nadin da aka yi wa Ogbobe na shekaru biyar ne kuma babu sabuntawa sannan za ta fara aiki nan take.

Ogbobe, kafin nadinsa, shine babban direkta na sashin fasahar sadarwa ta zamani, ICT, a kwamitin amintattu na NBTI.

Ogbobe yana da digirin digirgir da digiri na biyu bangaren Mechatronics Engineering da Mechanics/production engineering kamar yadda aka jero su.

Yana kuma wallafa bincike a guda 29 a mujallun Najeriya da kasashen waje, sannan ya samu kyaututuka da lambobin yabo da dama a baya.

2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu

A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ni masoyin Arewa ne, zan lallasa Atiku a 2023, 'yan Adamawa ni za su zaba, inji Okorocha

Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.

Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel