Dakarun MNJTF Sun Kashe 'Yan Boko Haram Da ISWAP 805 Da 'Yan Bindiga 5 a Benue

Dakarun MNJTF Sun Kashe 'Yan Boko Haram Da ISWAP 805 Da 'Yan Bindiga 5 a Benue

  • Dakarun sojoji na MNJTF sun yi nasarar kashe yan ta'addan Boko Haram 805, sun kuma ceto mutane fiye da 3,000
  • Kwamandan MNJTF, Manjo Janar Abdul-Khalifa Ibrahim ne ya bayyana haka a hedkwatar rundunar da ke N'Djamena
  • Sojojin Najeriya karkashin atisayen Operation Whirl Stroke su kuma sun yi nasarar kashe wasu da ake zargin yan bindiga ne su biyar a Benue

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Dakarun hadin gwiwa na kasashe masu yaki da Boko Haram, MNJTF, sun kashe yan Boko Haram/ISWAP guda 805 yayin wani atisaye na kawar da yan ta'addan da aka fara a watan Maris din wannan shekarar.

Ta ce ta bullo da sabbin dabaru na yaki da ta'addanci hakan yasa ta samu wannan nasarorin cikin wannan lokacin, rahoton The Punch.

Dakarun MNJTF Sun Kashe 'Yan Boko Haram Da ISWAP 805 Da 'Yan Bindiga 5 a Benue
Dakarun MNJTF Sun Halaka 'Yan Ta'adda 805 Da 'Yan Bindiga 5 a Benue. Hoto: @Mobile_Punch.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Yadda Abdulaziz Yari ya hada-kai da Akanta-Janar da wasu, aka wawuri kudin jihohi 9

Kwamandan MNJTF, Manjo Janar Abdul-Khalifa Ibrahim, ya ce atisayen ya kunshi sojojin kasa, na ruwa da sojojin sama a kokarinsu na fatattakar yan ta'addan ISWAP/Boko Haram da ke buya a yankin Tafkin Chadi.

Ya yi jawabi ne a hedkwatar MNJTF da ke N'Djamena, Jamhuriyar Chadi.

Kwamandan ya ce dakarun Nijar, Najariya, Chadi, Kamaru da Jamhuriyar Benin ne suka yi atisayen tare.

"Mun yi atisaye daban-daban a baya da ya bamu damar zuwa inda ba baya ba mu iya zuwa. Mun kashe bata gari da dama kuma hadin gwiwa da sojojin sama ya taimaka.
"Abin da muka yi ya tamaka mutane sun samu daman zirga-zirga; an fara kasuwanci; mutane sun fara komawa kauyukansu, kuma mutanen sun fara samun kwarin gwiwa.
"A yayin atisayen na Desert Sanity, mun kai hare-hare 17, inda muka kashe yan ta'adda 805 kuma fiye da 4,000 sun mika wuya. An kuma ceto fiye da mutane 3,000 da ke tsare," wani sashi na jawabin Ibrahim.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Kwana Kadan Zaben Fidda Gwani Na Yan Takarar Shugaban Kasa a APC

Ya yi kira ga gwamnatocin kasashen da ke atisayen su cigaba da bada gudunmawa na kayan zirga-zirga da makamai na zamani don karfafa wa sojojin gwiwa.

Ibrahim ya shawarci sauran yan ta'addan su rungumi zaman lafiya su ajiye makamansu.

Tafkin Chadi ya zama filin daga tun lokacin da ta'addanci ya fara a yankin.

Sojojin Najeriya sun kashe yan bindiga 5 a Benue

Hakazalika, Dakarun Operation Whirl Stroke sun kashe wasu da ake zargin yan ta'adda ne su biyar a karamar hukumar Katsina Ala a Jihar Benue.

Sai dai yan bindigan sun kashe wani mai gadi.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata da Alhamis lokacin da yan bindigan suka kai hari a kauyen Ayaghi.

Mai bawa Gwamna Ortom na Benue shawara a bangaren tsaro, Lt Col Hemba (mai ritaya) ne ya sanar da hakan a ofishinsa a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel