Malaman Qadiriyya da wasu kungiyoyi sun gana da Osinbajo, sun ce masoyin 'yan Najeriya ne

Malaman Qadiriyya da wasu kungiyoyi sun gana da Osinbajo, sun ce masoyin 'yan Najeriya ne

  • Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya karbi bakuncin wata tawaga mai karfi a fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • Tawagar dai ta kunshi limamai da malaman addinin musulunci da shuwagabannin musulmai daga sassan kasar nan
  • A yayin ziyarar, Osinbajo ya bukaci jiga-jigan na addini da na siyasa da su kara daukar kaimi wajen tabbatar da zaman lafiya da sauye-sauye masu kyau a cikin al’umma

Aso Rock - Wasu limamai, malaman addinin Islama, da shugabannin matasa a ranar Alhamis, 31 ga watan Maris sun ziyarci mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa dake Abuja.

Da yake karbar bakuncinsu, Osinbajo ya bayyana cewa hadin kai da hakuri sune muhimman dabi’un da ake bukata domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin al'umma mai addinai daban-daban kamar Najeriya.

Kara karanta wannan

APC ta shiga cikin hargitsi da Sanata Adamu su ka zama shugabannin jam’iyya na kasa

Osinbajo ya gana da malaman addini
Limamai Da Malaman Addinin Musulunci Sun Ziyarci Osinbajo, Sun Ce Yana Son Dukkan ‘Yan Najeriya | Hoto: Government of Nigeria
Asali: Twitter

Tawagar malaman da shuwagabannin kungiyoyi sama da 25 sun fito ne daga manyan cibiyoyin addini; majalisar malamai ta kasa, kungiyar Qadiriyya, Fitiyanul Islam ta Najeriya, Darikar Dariya, da majalisar matasan musulmi ta kasa.

Sauran sun hada da kungiyar dalibai musulmi ta Najeriya, Jammat Tajdidul Islamy, Salafiyya Youth Movement, Limamai na masallacin tarayya, da unguwar 'yan majalisu dake Apo, Abuja.

Tawagar ta samu jagorancin Farfesa Siraj Abdulkarim daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ci gaban al’umma da ci gaban matasa na kasa, kungiyar malamai ta kasa.

A lokacin da yake karbar bakin nasa, Farfesa Osinbajo ya bayyana jin dadinsa da zuwan tawagar inda ya ce:

"Ba kullum mutum ke samun daraja irin wannan ziyarar ba."

Mataimakin shugaban kasar ya bukaci mambobin tawagar da su ba da shawarar hanyoyin da kasar za ta samu hadin kai.

Kara karanta wannan

Tinubu @ 70: Buhari ya tura masa sakon taya murna, ya fadi halayen Tinubu na kirki

Da yake mayar da martani, Farfesa Abdulkarim ya bayyana cewa dole ne a kawar da hamayyar ba gaira ba dalili tsakanin Kirista da Musulmi, ya kuma yi kira ga Osinbajo da ya bullo da wani shiri na kara fahimtar juna da hadin kai.

Ya kuma yi kira da a kara zage damtse wajen yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Buhari ke yi a kasar.

Hotuna daga fadar shugaban kasa sun bayyana lokacin ganawar tasu:

IBB ya gana da 'yan takarar shugaban kasa 4 daga yankin Arewa

A wani labarin, tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya yi wata tattaunawa tare da yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) su hudu.

Sun yi ganawar ne a kokarinsu na ganin sun tsayar da dan takarar shugaban kasa guda daya bisa yarjejeniya gabannin zaben 2023, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gabanin zaben 2023: Tinubu ya ba jami'a kyautar N1bn ana tsaka da yajin aikin ASUU

Yan takarar hudu sune Dr. Bukola Saraki, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da Mohammed Hayatudeen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel