APC ta shiga cikin hargitsi da Sanata Adamu su ka zama shugabannin jam’iyya na kasa

APC ta shiga cikin hargitsi da Sanata Adamu su ka zama shugabannin jam’iyya na kasa

  • Jam’iyyar APC mai mulki ta zabi sababbin shugabanninta na kasa a karshen makon da ya wuce
  • Abdullahi Adamu da Abubakar Kyari su na da kujera a majalisa kafin zamansu shugabanni na kasa
  • Wannan ya sa wasu su ke ganin akwai bukatar Sanatocin su yi murabus, su ji da aikin jam’iyya

Abuja - Jam’iyyar APC ta samu kan ta a cikin hargitsi bayan zaben shugabanni na kasa da aka shirya. Jaridar Daily Trust ta bayyana haka a wani rahoto.

Hakan na zuwa ne a sakamakon zaben wasu shugabannin jam’iyya da aka yi alhali su na rike da wani matsayin mai kama da wadanda suka samu a yanzu.

Baya ga zaman Abdullahi Adamu da Abubakar Kyari shugabannin jam’iyya na kasa, yanzu haka Sanatocin APC ne masu-ci a majalisar dattawan kasar nan.

Kara karanta wannan

Duk da ‘Dan takararsa bai yi nasara ba, Tinubu ya taya Adamu murnar zama Shugaban APC

Tun 2011 Abdullahi Adamu yake majalisar tarayya a matsayin Sanatan jihar Nasarawa ta yamma.

A gefe guda kuma Sanata Abubakar Kyari yana wakiltar mutanen Arewacin jihar Borno a majalisar dattawa. Tun 2015 yake rike da wannan mukami.

Lauyoyi su na ta fashin baki

Jaridar ta ce biyo bayan zaben da aka yi, lauyoyi sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan batun.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Farfesa Paul Ananaba (SAN) ya ce babu dokar da ta ce Sanata ba zai iya hada aikinsa da wani aikin na dabam ba, amma zai fi dacewa dai su yi murabus.

A sashe na 183 na dokar kasa, gwamnan jiha ne aka haramtawa yin wannan aiki a lokacin da yake rike da kujerarsa. Dokar ba ta shafi aikin ‘dan majalisa ba.

Duk da haka Ananaba wanda babban lauya ne kuma masanin shari’a, ya ce sam ba zai yiwu a iya hada nauyin jagorantar jam’iyya irin APC da aikin Sanata ba.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar Buhari ya dauko ‘Dan takaran da zai ba kowa mamaki, ya mara masa baya

Femi Falana (SAN) ya ce jam’iyyun PDP da APC sun raina jama’a, kuma za su kalubalance su.

Amma Dayo Akinlaja (SAN) yana ganin ba a saba wata doka ba domin shugaban kasa da gwamnoni aka hana su ci wani albashi dabam da na aikinsu.

'Yan PDP sun ce ba haka ba

Sanata Enyinnaya Abaribe a madadin Sanatocin PDP a majalisar dattawa ya ce ya kamata abokan aikin na sa su ajiye mukamansu domin su ji da jam’iyyar APC.

Rahoton ya ce wannan shi ne ra’ayin jam’iyyar hamayya ta PDP. Amma INEC ta ce akwai matakan da ake bi kafin a maye gurbin wani a majalisar tarayya.

Adamu zai jagoranci NWC

An san a zaben da aka gudanar a makon da ya gabata, Adamu ne ya zama shugaban APC na kasa. Kyari kuma ya tashi da kujerar mataimakinsa na shiyyar Arewa.

Legit.ng Hausa ta fahimci ba su biyu kadai ke da mukami ba. Sabon mai bada shawara a kan shari’a, Ahmad El-Marzuk shi ne kwamishinan shari’an Katsina.

Kara karanta wannan

Jerin shugabannin da suka yi nasara, da wadanda suka sha kasa a zaben jam’iyyar APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel