Tinubu @ 70: Buhari ya tura masa sakon taya murna, ya fadi halayen Tinubu na kirki

Tinubu @ 70: Buhari ya tura masa sakon taya murna, ya fadi halayen Tinubu na kirki

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, jigon jam’iyyar APC kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, zai cika shekaru 70 a ranar Talata, 29 ga Maris
  • Gabanin bikin zagayowar ranar haihuwarsa, shugaba Buhari Buhari ya fitar da sanarwar taya murna ga tsohon gwamnan jihar Legas
  • Shugaban ya jinjinawa jajircewa, juriya, rashin nuna son kai da martabar Tinubu wajen fifita jin dadin al’umma da hadin kan al’umma sama da son rai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun ‘ya’yan APC da shuwagabanninta wajen taya jagoran jam’iyyar na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekaru 70 da haihuwa a ranar 29 ga Maris, 2022.

Shugaban kasar, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin ta hannun mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya tabbatar da irin gudunmawar da jigon na APC ke bayarwa ga ci gaban siyasa, tattalin arziki da zamantakewar kasar nan.

Kara karanta wannan

Gabanin zaben 2023: Tinubu ya ba jami'a kyautar N1bn ana tsaka da yajin aikin ASUU

Buhari ya tura sakon taya murna ga Tinubu yayin cika shekaru 70
Tinubu @70: Buhari ya tura masa sakon taya murna, ya fadi halayen Tinubu na kirki | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa, Buhari ya kuma yaba da jajircewarsa, juriyarsa, rashin nuna son kai da martabarsa a ko da yaushe yana fifita hadin kan al’umma sama da son kai.

Hakazalika, tare da samun goyon baya da hangen nesan Nijeriya mai girma ta hanyar zuba jari ga mutane, hukumomi da gwamnatoci, ba tare da tunanin kabilanci ko akida ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma yi addu’ar Allah ya karawa Asiwaju Tinubu, Jagaban Masarautar Borgu karfi da lafiya da hikima domin ya ci gaba da yi wa kasa hidima da kuma bil’adama baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel