Yanzu-Yanzu: IBB ya gana da 'yan takarar shugaban kasa 4 daga yankin Arewa

Yanzu-Yanzu: IBB ya gana da 'yan takarar shugaban kasa 4 daga yankin Arewa

Tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya yi wata tattaunawa tare da yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) su hudu.

Sun yi ganawar ne a kokarinsu na ganin sun tsayar da dan takarar shugaban kasa guda daya bisa yarjejeniya gabannin zaben 2023, Leadership ta ruwaito.

IBB ya gana da 'yan Arewa masu neman gaje Buhari
Yanzu-Yanzu: IBB ya gana da 'yan takarar shugaban kasa 4 daga yankin Arewa | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Yan takarar hudu sune Dr. Bukola Saraki, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da Mohammed Hayatudeen.

Jiga-jigan na PDP sun kasance a gidan IBB da ke hilltop a garin Minna, babban birnin jihar Neja ba tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ba, wanda shima dan takarar kujerar shugaban kasar ne.

Tsohon shugaban kasar ya goyi bayan hukuncin tsayar da dan takaKar yarjejeniya a tsakanin masu takarar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Mai son gaje kujerar Buhari daga PDP ya hakura, ya barwa Peter Obi

Karin bayani nan tafe..

Asali: Legit.ng

Online view pixel