Rudani: 'Yan majalisun jiha guda uku sun yi murabus, ana neman masu maye gurbinsu

Rudani: 'Yan majalisun jiha guda uku sun yi murabus, ana neman masu maye gurbinsu

  • A halin yanzu dai babu wanda ke kan kujeru uku ta ‘yan majalisar PDP na majalisar dokokin jihar Ebonyi
  • Kujerun ‘yan majalisar na PDP, na Ali Okechukwu, Franca Okpo Abakaliki da kuma Victor Aleke an bayyana su a matsayin wadanda ba kowa akai a ranar Talata
  • Kakakin majalisar, Francis Ogbonna Nwifuru ya karanta wasikun murabus din tsoffin ‘yan majalisar a zaman da suka yi a ranar Talata

Abakaliki, Ebonyi - ‘Yan majalisar dokokin jihar Ebonyi uku da ke jam’iyyar PDP a ranar Talata 15 ga watan Maris sun yi murabus.

Hakan ne ya sa majalisar jihar ta bayyana kujerunsu a matsayin wadanda babu kowa a kai a zauren majalisar da ‘yan majalisar wakilai 15 na jam’iyyar APC suka halarta a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Kalubalen da bangaren su Shekarau za su fuskanta a siyasa kafin zaben 2023

'Yan Majalisa sun aje aiki
Rudani: 'Yan majalisun jiha guda uku sun yi murabus, ana neman masu maye gurbinsu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

'Yan majalisun da suka yi murabus

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, duk da cewa ‘yan majalisar na PDP ba su halarci zaman ba, amma an bayyana sunayensu kamar haka:

  1. Ali Okechukwu (Ishielu ta Arewa)
  2. Franca Okpo (Abakaliki ta Arewa)
  3. Victor Aleke (Ebonyi ta Yamma).

Bayan sanarwar, kakakin majalisar Francis Ogbonna Nwifuru ya umurci magatakarda da ya sanar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan batun kuma ana bukatar gudanar da sabon zabe a mazabun da abin ya shafa.

Ku tuna cewa a ranar 8 ga Maris, 2022, wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta kori kakakin majalisar jihar Ebonyi da wasu ‘yan majalisa 15 saboda sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC a jihar, inji Vanguard.

Kara karanta wannan

Wani shahararren dan siyasar arewa ya fice daga APC, ya bayyana dalilinsa

Gwamna ya sallami baki daya kwamishinoni da hadiman gwamnatinsa daga aiki

A wani labaarin, gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya sanar da rushe baki ɗaya mambobin kwamitin zartarwa na gwamnatinsa da duk wasu hadimai.

Daily Trust ta rahoto cewa wannan mataki zai fara aiki ne daga ranar 16 ga watan Maris, na wannan shekarar da muke ciki 2022.

Gwamanan ya yi haka ne domin fara shirye-shiryen miƙa ragamar mulki ga sabuwar gwamnatin Farfesa Charles Soludo ranar 17 ga watan Maris, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel