Gwamna ya sallami baki ɗaya kwamishinoni da hadiman gwamnatinsa daga aiki

Gwamna ya sallami baki ɗaya kwamishinoni da hadiman gwamnatinsa daga aiki

  • Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya sanar da rushe baki ɗaya mambobin kwamitin zartarwa na gwamnatinsa
  • Gwamnan ya ɗauki matakin ne yayin da yake shirin miƙa nulki ga sabuwar gwamnati karkashin zababben gwamna
  • A ranar 16 ga watan Maris, 2022 Gwamna Obiano zai miƙa ragamar jagorancin Anambra a hannun sabon gwamna, Farfesa Soludo

Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya sanar da rushe baki ɗaya mambobin kwamitin zartarwa na gwamnatinsa da duk wasu hadimai.

Daily Trust ta rahoto cewa wannan mataki zai fara aiki ne daga ranar 16 ga watan Maris, na wannan shekarar da muke ciki 2022.

Gwamanan ya yi haka ne domin fara shirye-shiryen miƙa ragamar mulki ga sabuwar gwamnatin Farfesa Charles Soludo ranar 17 ga watan Maris, 2022.

Kara karanta wannan

Jerin yadda Sojoji 18, yan sanda 6 da yan Najeriya 76 suka rasa rayukansu cikin mako daya

Gwamna Obiano
Gwamna ya sallami baki ɗaya kwmaishinoni da hadiman gwamnatinsa daga aiki Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Gwamna Obiano, a ranar mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Anambra, Farfesa Solo Chukwulobelu, ya roki hadimai da mambobin majalisar da su mika ragamar ma'aikatunsu ga manyan jami'ai.

Ana tsamnanin Obiano zai miƙa mulki ga gwamna mai jiran gado, Farfesa Soludo a ranar 17 ga watan Maris, bayan kammala zango biyu, shekara 8 a kan mulki.

Waɗan da matakin gwamna Obiano ya shafa

A cewar sanarwan, waɗan da lamarin ya shafa ya haɗa baki ɗaya naɗe-naɗen siyasa da suka haɗa da, Sakataren gwamnati, shugaban ma'aikata, Sakatarorin gwamna, sakataren watsa labarai da kwamishinoni.

Sauran sune mashawarta na musamman, shugabannin kwamitoci, hukumomi, manyan mataimaka na musamman, da mataimaka na musamman.

The Nation ta rahoto Sanarwan ta ce:

"Muna mai sanar da dukkan masu rike da nukaman siyasa cewa wa'adin wannan gwamnatin ya kare ranar 16 ga watan Maris. Bisa haka duk wani da aka naɗa lokacin sa ya zo ƙarshe a wancan rana."

Kara karanta wannan

Gwamna Matawalle ya gargaɗi gwamnoni abu daya game da rikicin shugabancin APC

"Bisa haka muna shawartan kowa ya mika ragamar ofishinsa ga babban ma'aikacin ma'aikatarsa, kuma kowane mutumi ya tabbata ya karɓi duk abin da ya dace."

Sanarwan ta ƙara da cewa lamarin bai shafi Daraktoci, da sakatarori da shugabannin kwalejin gwamnatin jiha ba har sai gwamna na gaba ya zo.

A wani labarin kuma Gwamoni jam'iyyar PDP biyu sun barke da rikici mai zafi, sun fara kiran juna 'Ma ci Amana'

Rikici tsakanin gwamnonin jam'iyyar PDP biyu ya kara tsananta, Wike ya kara mauda wa Obaseki martani mai zafi.

Wike ya roki tsohon shugaban APC na ƙasa gafara bisa kin ɗaukar gargaɗinsa game da halayen gwamna Obaseki na Edo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel