Rikicin APC: Kalubalen da bangaren su Shekarau za su fuskanta a siyasa kafin zaben 2023

Rikicin APC: Kalubalen da bangaren su Shekarau za su fuskanta a siyasa kafin zaben 2023

  • Ana shari’a tsakanin bangaren Ibrahim Shekarau da Barau Jibrin da tsagin Gwamnatin Ganduje
  • Rikicin ya kai gaban kotun koli alhali lokacin shirya zabukan fitar da gwani ya na neman ya kure
  • Hakan zai iya jawo a samu manyan bangarori uku da za su yi takara a jihar Kano a zabe mai zuwa

Kano - Wani rahoto da Daily Trust ta fitar ya nuna cewa lokaci yana neman ya kurewa bangaren taware na Ibrahim Shekarau a rikicin cikin gida na APC.

Kamar yadda ku ka samu rahoto kwanakin baya, hukumar INEC ta bukaci duka jam’iyyun siyasa su yi zaben tsaida ‘dan takara zuwa 3 ga watan Yunin 2022.

Kafin nan kuma ana sa ran APC ta gudanar da zaben shugabanni a ranar 26 ga watan Maris. A halin yanzu an rantsar da bangaren Abdullahi Abbas a Kano.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasa 6 da za su iya bayyana shirin takarar shugaban kasa nan da kwanaki masu zuwa

Mai magana da yawun bakin shugaban G7, Dr. Sule Ya’u Sule ya shaidawa manema labarai cewa kan jagororin ‘yan tawaren na jam’iyyar APC a dunkule yake.

Dr. Ya’u Sule ya ce su na sa ran kotun koli ta zartar da hukuncin da zai yi masu dadi kwanan nan. Amma shi ma ya nuna su na da wasu zabin a kasa bayan APC.

Rikicin APC
Manyan APC da 'Yan siyasar Kano Hoto: @BuniMedia
Asali: Twitter

Karbe jam’iyyar PDP

Jaridar ta ce shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya gana da Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Shekarau. Hakan ya nuna akwai yiwuwar sake komawarsa PDP.

A ‘yan kwanakin nan an ji jagororin Kwankwasiyya masu shirin zama a PDP sun hadu da Shekarau. Idan an dace, G7 za su iya sauya-sheka, su karbe PDP.

Sauya-shekar Kwankwaso

Shekarau da sauran ‘yan tafiyar G7 za su karbe rikon PDP ko su mamaye ta ne idan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yarda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Makusantan Kwankwaso sun lallaba sun gana da Shekarau, suna kokarin sake jawo shi PDP

Muddin Rabiu Kwankwaso ya yi zamansa a PDP, zai yi wa Shekarau, Barau Jibrin da sauran masu rikici da Ganduje wahalar samun wurin zama a jam’iyyar adawar.

Kuma hakan zai shafi Sanata Barau Jibrin da Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada da suke harin gwamna. Za su gamu da kalubale daga mutanen Amb. Aminu Wali.

Hakuri da APC

Wani malami da yake koyar da ilmin siyasa a jami’ar Bayero da ke Kano, Dr. Aminu Hayatu ya na ganin abin da ya fi dacewa da ‘Yan G7 shi ne su yi zamansu a APC.

Hayatu yana da ra’ayin cewa idan uwar jam’iyya ta sa baki, aka yi sulhu, wasu ‘yan tawaren za su iya samun takara. Amma babu tabbacin za ayi hakan a zabe na 2023.

Zaben Kano a 2023

Idan aka ja daga tsakanin APC, PDP da NNPP, zai zama karon farko a jihar Kano da Kwankwaso, Shekarau da kuma Ganduje duk suka yi takara a jam’iyyu dabam.

Kara karanta wannan

Yadda Mai Mala Buni da shugabannin APC suke fama da shari’a fiye da 200 a gaban kotu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng