'Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban ASUU na Jami'ar Gusau, sun sace 'yan uwansa 5 da makwabcinsa

'Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban ASUU na Jami'ar Gusau, sun sace 'yan uwansa 5 da makwabcinsa

  • 'Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban ASUU na Jami'ar Tarayya da ke Gusau, sun sace yan uwansa 5 da makwabcinsa
  • Abdurrahman Adamu, Shugaban ASUU na FUGUS ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce kawo yanzu ba a kira shi batun biyan fansa ba
  • Wani dan uwan shugaban na ASUU kuma ma'aikacin Jami'ar Gusau shima ya magantu kan harin yana mai cewa Adamu bai kwana a gidansa ba a ranar

Jihar Zamfara - Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, ta Jami'ar Tarayya da ke Gusau, FUGUS, Mr Abdurrahman Adamu, Channels Television ta ruwaito.

A cewar bayanai da aka tattaro, an sace mutane shida yayin harin da aka kai a gidan shugaban ASUUn da ke Damba Quaters, a wajen Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Gwamna ya ko'da kansa, ya ce shi kadai ya cancanci kujerar Buhari a 2023

Da Dumi-Dumi: 'Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban ASUU na Jami'ar Gusau, sun sace mutane 6
Mahara sun kutsa gidan shugaban ASUU na Jami'ar Gusau, sun sace 6. Hoto: Channels TV
Asali: Twitter

Wani ma'aikacin jami'ar kuma dan uwan shugaban na ASUU ya shaida wa Channels Television cewa yan bindigan sun afka gidan Adamu ne a safiyar ranar Laraba sannan suka sace mutane biyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu garkuwar sun sace wani makwabci, wanda shima ma'aikaci ne a sashin kula da biyan kudade na jami'ar.

Majiyar ta kara da cewa shugaban na ASUU bai kwana a gida ba a ranar Talata, don haka baya nan a lokacin da aka kai harin.

Wadanda aka sace a gidan shugaban ASUUn sun hada da kaninsa, yar kaninsa, dan kaninsa da kannen matansa biyu.

Majiyar ta ce:

"Su biyar da wani Abbas Umar wanda makwabcinsa ne kuma ma'aikacin sashin kula da kudade a Jami'ar Tarayya ta Gusau."

Adamu ya magantu game da harin

Da aka tuntube shi domin ji ta bakinsa, Adamu ya bayyana cewa an yi kaca-kaca da gidansa, ya kara da cewa an sace kayayyaki da dama.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan awaren IPOB suka halaka makiyayi, suka bindige shanu 30

Ya tabbatar da cewa an sace yan uwansa, ya yi bayanin cewa babu wanda ya yi kokarin taka wa maharan birki.

Ya kara da cewa yan sanda sun iso gidansa ne da safe, suka yi wasu tambayoyi suka tafi. A cewarsa, har yanzu maharan ba su tuntubi shi ko iyalansa ba don biyan kudin fansa.

Yan sanda ba su tabbatar da harin ba

Kawo yanzu, yan sanda ba su riga sun tabbatar da sace mutanen ba. Da aka tuntube shi, kakakin yan sanda, Mohammed Shehu ya ce zai bincika ya ji ba'asi kafin ya bada cikakken bayani.

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu

Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel