An kuma: An sake yin garkuwa da wani basaraken gargajiya a jihar Filato

An kuma: An sake yin garkuwa da wani basaraken gargajiya a jihar Filato

  • Bayan sace wani basaraken gargajiya a jihar Filato, an sake sace wani sarki a yankin Filato ta Kudu a jihar
  • Ya zuwa yanzu, ba a san mutanen da suka sace shi ba, sannan basu kira waya don bayyana me suke bukata ba
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma bayyana matakan da take dauka domin kubutar dashi

Jihar Filato Wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance ko su wanene ba sun yi garkuwa da Hakimin Vwang da ke karamar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato, Da Gyang Balak Gut, Channels Tv ta rahoto.

Mista Gut, wanda shi ne mai sarautar Da Gwom Rwei na garin Vwang, an ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kama shi a daren Lahadi a lokacin da yake komawa gida a Vom, da ke ‘yan mitoci a kofar shiga Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru ta Kasa (NIPSS).

Kara karanta wannan

Daga karshe: An sako shugaban ASUU da tsohon dan takarar gwamna da aka sace

Ans sace sarkin gargajiya a Jos
An kuma: An sake yin garkuwa da wani basaraken gargajiya a jihar Filato | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Daga bisani an dauke shi zuwa wani wuri da ba a sani ba, kuma babu wanda ya san ko su wanene maharan da kuma ko za su bukaci kudi kamar yadda aka saba a baya-bayan nan.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, Gabriel Ubah, a lokacin da yake bayyana faruwar lamarin, ya bayyana cewa Kwamishinan ‘yan sandan Bartholomew Onyeka da manyan jami’an ‘yan sanda sun ziyarci wurin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, ya ce an tattara jami’an tsaro don bin diddigin wadanda suka yi garkuwa da basaraken tare da ba da umarnin kubutar dashi cikin koshin lafiya.

Gundumar Vwang da ke karamar hukumar Jos ta Kudu ce ke da Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabarun (NIPSS), Cibiyar Nazarin Dabbobi ta Kasa (NVRI), da Kwalejin Kimiyyar Kasa da dai sauransu.

Sace Gwom Rwei na zuwa ne bayan wata guda da sace wani basaraken gargajiya a jihar, Charles Mato Dakat.

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Sai dai an sako Dakat, wanda shine babban sarkin Gindiri a karamar hukumar Mangu kwanaki biyar bayan sace shi, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi ‘yan uwansa kwanaki bayan sun yi garkuwa da shi, inda suka bukaci a biya shi kudin fansa naira miliyan 500 kafin su sako sarkin.

Duk da haka, ba a bayyana ba ko an biya kudin fansa; Har ila yau, ba a san irin rawar da jami'an tsaro suka taka wajen sakin basaraken ba.

'Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Basarake a jihar Filato

A wani labarin, wasu tsagerun 'yan bindiga sun yi awon gaba da, Charles Mato Dakat, babban basarake mai daraja ta daya a garin Gindiri, karamar hukumar Mangu, jihar Filato.

Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun samu nasarar sace sarkin ne bayan bude wuta kan mai uwa da wabi a gidansa da sanyin safiyar Lahadin nan.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bayan watanni 6, an sako daliban kwalejin da aka sace a Kebbi

Helen Bulus, wacce ke zaune a yankin masarautar Dakat, tace lamarin ya faru da misalin karfe 2:00 na safiyar Lahadi, kuma maharan sun zo da yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel