Da dumi-dumi: Bayan watanni 6, an sako daliban kwalejin da aka sace a Kebbi

Da dumi-dumi: Bayan watanni 6, an sako daliban kwalejin da aka sace a Kebbi

  • Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar sakin dalibai 30 da 'yan bindiga suka sace watanni shida da suka gabata
  • Idan baku manta ba, an sace dalibai da dama a wata kwalejin gwamnati da ke Yauri a jihar Kebbi ranar 17 ga watan Yuni, 2021
  • Gwamnati ta ce a yanzu haka daliban na hannunta, kuma za ta binciki lafiyarsu sannan a mika su ga danginsu

Kebbi - Rahoton Daily Trust ya ce, dalibai 30 na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi da kuma malami daya na makarantar, sun samu ‘yanci bayan watanni shida da aka yi garkuwa da su.

A ranar 17 ga watan Yuni, 2021, wasu ‘yan bindiga daga dajin Rijau da ke makwabtaka da jihar Neja, sun kutsa cikin makarantar tare da yin garkuwa da dalibai da ma’aikata.

Gwamnan Kebbi ya tabbatar sakin dalibai 30 na Yauri
Da dumi-dumi: Bayan watanni 6, an ceto daliban kwalejin da aka sace a Kebbi | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

‘Yan bindigar wadanda rahotanni suka ce sun mamaye makarantar ne a kan babura, sun yi fatattaki jami’an tsaron da ke wurin, inda suka kashe dan sanda nan take.

Gwamna Atiku Bagudu na Kebbi ya yi watsi da tattaunawa da ta'addan da ke neman kudin fansa.

Watanni hudu bayan sace su, an sako malamai uku da dalibai 30 amma babu tabbas ko an biya kudin fansa.

A ranar Asabar din da ta gabata ne mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai Yahaya Sarki ya tabbatar da sakin wasu dalibai 30 da malaminsu.

“A yau Asabar 8 ga watan Janairu, 2022 dalibai 30 na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri da malami daya sun isa Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi bayan an sako su. Za a duba lafiyarsu tare da tallafa musu kafin daga bisani a sake hada su da iyalansu.

“Za a iya tunawa a ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba, 2022, an sako daliban makarantar guda 30, aka kawo su Birnin Kebbi domin a sada su da iyalansu.
"Muna godiya ga dukkan hukumomin tsaro da wadanda suka taimaka wajen ganin an sako su, yayin da muke taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar nasarar da aka samu."

Ya zuwa yanzu, an sako dalibai 57 da malaman kwalejin 4, inda aka tara da wadanda aka sako a watan Oktoba, kamar yadda The Guardian ta rahoto.

Yawan hare-haren da ake kaiwa ya zama abin damuwa ga 'yan Najeriya ganin yadda kungiyoyin 'yan ta'adda ke kai hare-hare a fadin kasar duk kuwa da kokarin da da gwamnati da jami'an tsaro suka ce suna yi.

A daya daga cikin irin wadannan hare-hare, 'yan bindiga masu gudun hijita sun kashe mutane sama da 143 a jihar Zamfara.

Tuni dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa wadanda abin ya shafa, inda ya sha alwashin cewa za a zakulo wadanda suka yi barnar.

Bayan kimanin kwanaki 120, Dogo Gide ya sako daliban Yauri 28 da malamansu biyu da ke hannunsa

A wani labarin, Kasurgumin dan bindiga, Dogo Gide, ya sako daliban makarantar sakandare na tarayya da ke Birnin Yauri, a ranar Laraba bayan sun shafe kwanaki a hannunsa, Daily Trust ta ruwaito.

An sace su ne kimanin watanni hudu a makarantarsu a lokacin da yan bindigan suka ci galaba kan jami'an tsaro a makarantarsu da ke wani kauye a jihar Kebbi.

Daily Trust ta ruwaito cewa an saki wasu daga cikin daliban a makon da ta gabata, bayan tattaunawa da wasu daga cikin iyayen yaran da suka ce an yi musu alkawarin sada su da yayansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel