Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Basarake a jihar Filato

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Basarake a jihar Filato

  • Da safiyar Lahadin nan, wasu miyagun ƴan bindiga sun sace babban sarki a yankin karamar hukumar Mangu, jihar Filato
  • Rahoto daga yankin ya nuna cewa maharam sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi, kafin daga bisani su tasa basaraken zuwa wani wuri
  • Rundunar Operation Safe Haven ta tura dakarun soji yankin, kuma sun bazama cikin jeji don ceto basaraken

Plateau - Wasu tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da, Charles Mato Dakat, babban basarake mai daraja ta ɗaya a garin Gindiri, ƙaramar hukumar Mangu, jihar Filato.

Dailytrust ta rahoto cewa maharan sun samu nasarar sace sarkin ne bayan bude wuta kan mai uwa da wabi a gidansa da sanyin safiyar Lahadin nan.

Helen Bulus, wacce ke zaune a yankin masarautar Dakat, tace lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na safiyar Lahadi, kuma maharan sun zo da yawa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Katafaren kantin 'Next Cash and Carry' da ke Abuja ya na ci da wuta

Yan bindiga
Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Basarake a jihar Filato Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Punch ta rahoto Helen tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sarki na cikin gidansa shi kaɗai saboda matarsa ta yi tafiya zuwa Jos kuma ƴaƴanssa ba sa nan lokacin. Duk da lokacin dare ne, amma karar harbin yan bindiga yasa mutane gudun tsira."
"Har sai da gari ya waye tangaran, sannan muka je gidan inda muka gane maharan sun yi awon gaba da sarkin."

Wane mataki aka ɗauka?

Ɗan majalisa mai wakiltar Mangu ta kudu a majalisar dokokin jihar Filato, Bala Fwangje, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa tuni aka tura jami'an tsaro zuwa yankin, kuma sun bazama cikin jeji domin nemo inda maharan suka yi da basaraken.

"Lamarin ba shi da daɗin ji, yanzun nan na tabbatar da abin da ya faru daga wasu jami'an tsaro."

Rundunar OPSH ta tabbatar

Kakakin rundunar sojin Operation Safe Haven dake kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankin, Manjo Ishaku Takwa, ya tabbatar da faruwar lamarin

Kara karanta wannan

Mutum 7 sun rasa rayukansu a mumunan hadarin da ya auku ranar Kirismeti

Ya ƙara da cewa tuni jami'an sojoji suka dira yankin, kuma suna cigaban da neman masu garkuwan domin ceto sarkin cikin koshin lafiya.

A wani labarin na daban kuma Muhimman abubuwa 4 da kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya nema a wasikar sulhu

Jagoran yan bindiga, wanda ake ganin ya addabi jihar Zamfara da wasu yankuna, Bello Turji, ya nemi a zauna zaman sulhu.

A cikin wasikar da ya aike wa shugaba Buhari, gwamna Matawalle, da sarkin Shinkafi, Turji ya nemi a cika wasu sharuɗɗa 4.

Asali: Legit.ng

Online view pixel