Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dadinsa ga yadda 'yan bindiga suka hallaka mutane da dama a Zamfara
  • Shugaban ya bayyana kokensa ne bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai, suka hallaka mutane sama da da 150
  • Ya jaddada manufar gwamnatinsa na cewa ba za ta lamunci hare-haren 'yan bindiga a yankin ba

Abuja - Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan da wasu ‘yan bindiga suka yi a wasu kauyuka a jihar Zamfara.

Shugaban kasar, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka samu rahotannin mummunan kisa a jihar.

Shugaban kasa ya yi Allah wadai da kashe mutane a Zamfara
Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Buhari, wanda ya yi kira ga al’ummar da abin ya shafa da su yi hakuri kan abin da ya faru, inda kuma yayi alkawarin mataki kan wadanda suka aikata barnar.

A sanarwar sa Bauhari Sallau ya yada daga Garba Shehu a shafin Facebook, shugaba Buhari ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Hare-hare na baya-bayan nan kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, da ‘yan bindiga ke kai wa, wani mataki ne na yankar kauna daga masu kisan gilla, a yanzu haka suna fuskantar kalubale daga sojojin mu da ke da kayan aikin da za su tunkari wadannan makiya bil’adama.
“A bisa kudurin da na dauka na tunkarar mummunan ta’addanci, ina tabbatar wa wadannan al’ummomin da aka yi wa barna da sauran ‘yan Najeriya cewa wannan gwamnati ba za ta yi watsi da su ga makomarsu ba domin mun fi kowane lokaci kudurin kawar da wadannan ’yan ta’adda.
"Wadannan 'yan ta'adda za su zama tarihi domin ba za mu yi kasa a gwiwa ba a ayyukan da muke yi na soja a halin yanzu don kawar da wadannan 'yan baranda da ke addabar mutanen da ba su ji ba su gani ba."

Gwamnatin Zamfara ta daura alhakin sabon harin jihar kan masu yiwa ‘yan bindiga kwarmato

A wani labarin, rahotanni sun kawo cewa yawan mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da yan bindiga suka kai kauyukan jihar Zamfara, a farkon makon nan ya tasar ma 200, The Cable ta rahoto.

A cewar jaridar Punch, wadanda suka tsallake rijiya da baya a harin sun ce 'yan bindiga sun kashe mazauna kauyuka su sama da 200 sannan suka kona gidaje da dama.

Da yake martani a kan harin, Ibrahim Dosara, kwamishinan labaran jihar Zamfara, ya dora alhakin hare-haren akan masu yiwa 'yan bindiga leken asiri, jaridar The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel