Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 15 a wani hari da suka kai jihar Neja

Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 15 a wani hari da suka kai jihar Neja

  • Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 15 a wani farmaki da suka kai kauyen Kulho a karamar hukumar Mashegu ta jihar Neja
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar Wasiu Abiodun, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 16 ga watan Janairu
  • Ya ce an tura jami'an rundunar domin gudanar da aikin bincike da ceto mutanen

Niger - A kalla mutane 15 aka yi garkuwa da su bayan wani hari da yan bindiga suka kai kan al'umman wani gari a jihar Neja.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 16 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

An kuma: An sake yin garkuwa da wani basaraken gargajiya a jihar Filato

Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 15 a wani hari da suka kai jihar Neja
Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 15 a wani hari da suka kai jihar Neja Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A cewar Abiodun, yan bindigar sun farmaki Kulho, wani kauye da ke kusa da yankin Ibbi a karamar hukumar Mashegu sannan suka yi garkuwa da mutane 15 a ranar 14 ga watan Janairu.

Ya ce maharan sun kuma farmaki Mashegu ta jihar Jigawa sannan suka yi awon gaba da wasu dabbobi da ba a tantance adadinsu ba a wannan rana.

A cewarsa, an zuba jami'an tsaro domin su gudanar da shirin bincike da kuma ceto wadanda lamarin ya ritsa da su, rahoton Premium Times.

Ya ce:

"Mun nemi taimakon mazauna yankin da su bayar da gudummawar ingantattun bayanai da za su taimaka wajen kama miyagun."

Buhari ya ba sojoji umurnin yin gaggarumin aiki a wata jihar Arewa

Ahalin da ake ciki, mun kawo a baya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci rundunar soji da dauki gagarumin mataki kan lamarin kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama mutumin da ake zargi da kwantawa da yar shekara 80 a Nasarawa

The Nation ta rahoto cewa Buhari ya kuma umurci sojojin da su yi amfani da karfi a tsarin kakkabe yan ta'ddan da suka addabi jihar.

Babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin labarai, Garba Shehu, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 16 ga watan Janairu, ya ce shugaban kasar ya bayar da umurnin ne ga hedkwatar tsaro, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel