Da dumi-dumi: Buhari ya ba sojoji umurnin yin gaggarumin aiki a wata jihar Arewa

Da dumi-dumi: Buhari ya ba sojoji umurnin yin gaggarumin aiki a wata jihar Arewa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci rundunar sojin kasar da ta dauki mataki kan kashe-kashe da garkuwa da mutane da ke gudana a jihar Neja
  • Buhari ya kuma bukaci rundunar da ta tabbatar da manufofin da aka tanada na amfani da karfi kan miyagun
  • Ya kuma yi jaje ga gwamnati da al'ummar jihar kan hare-haren yan ta'adda a yankin

Niger - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci rundunar soji da dauki gagarumin mataki kan lamarin kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Neja.

The Nation ta rahoto cewa Buhari ya kuma umurci sojojin da su yi amfani da karfi a tsarin kakkabe yan ta'ddan da suka addabi jihar.

Babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin labarai, Garba Shehu, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 16 ga watan Janairu, ya ce shugaban kasar ya bayar da umurnin ne ga hedkwatar tsaro, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Katsina: Masari ya yi umarnin bude dukkan gidajen mai da kasuwannin shanu a jihar

Da dumi-dumi: Buhari ya ba sojoji umurnin yin gaggarumin aiki a wata jihar Arewa
Da dumi-dumi: Buhari ya ba sojoji umurnin yin gaggarumin aiki a wata jihar Arewa Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Ya ce a matsayinsa na babban kwamandan tsaro a kasar, Buhari ya shirya wani gagarumin aiki na soji a jihar Neja wacce ke ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da na ragowar ‘yan ta’addan Boko Haram da ke tserewa daga yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin kasar.

A sakonsa zuwa ga gwamnati da mutanen jihar Neja, shugaba Buhari ya ce:

"Ina so in nuna tausayawa na ga gwamnati da al’ummar jihar sakamakon matsalolin tsaro da suka faru a baya-bayan nan."

Shugaban kasar ya jadadda cewa tsaro hakki ne na kowani dan kasa kuma ta hanyar ba hukumomin doka cikakken goyon baya da hadin kai "za mu iya magance matsalolin".

Sanarwar ta kara da cewa:

"A shirye gwamnatin tarayya take ta karfafa goyon baya da hadin kai ga dukkan jihohi. Na yi imanin cewa da cikakken hadin kan ‘yan kasa, shakka babu za mu shawo kan wannan matsala."

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi martani kan kyautar da Tinubu ya bayar na N50n ga 'yan Zamfara

Yadda 'yan ta'adda suka bindige mutane 13 har lahira a harin Jihar Neja

A baya mun ji cewa ana samun bayanai akan yadda ‘yan bindiga suka kai farmaki wasu anguwanni da ke cikin karamar hukumar Shiroro a cikin jihar inda suka halaka fiye da mutane 13 a Nakundna da Wurukuchi ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.

Harin ya auku ne duk da yadda jami’an tsaro suke ci gaba da sintiri a wasu kauyaku da ke Shiroro da sauran kananun hukumomin da ta’addanci ya addaba a jihar.

Harin ranar Talata ya auku ne bayan bai wuce makonni biyu ba da ‘yan bindiga suka kai wa ma’aikatan Zungeru Dam farmaki har suka halaka mutane biyu sannan suka yi garkuwa da wasu ‘yan China guda biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel