Yan sanda sun kama mutumin da ake zargi da kwantawa da yar shekara 80 a Nasarawa

Yan sanda sun kama mutumin da ake zargi da kwantawa da yar shekara 80 a Nasarawa

  • Jami'an yan sanda sun yi ram da wani mutum mai suna Dan'asabe Ebbo kan zargin lalata da tsohuwa yar shekara 80
  • Mutumin ya afkawa tsohuwar ne a gidanta da ke kauyen Kundami da ke Garaku, karamar hukumar Lokonga na jihar Nasarawa
  • Kakakin yan sandan jihar ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi, 16 ga watan Janairu

Nasarawa - Rundunar yan sanda a jihar Nasarawa ta kama wani mutum mai shekara 43 bisa zarginsa da haikewa tsohuwa yar shekara 80 a jihar.

Rundunar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinta, Ramhan Nansel, a ranar Lahadi, 16 ga watan Janairu, jaridar Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 15 a wani hari da suka kai jihar Neja

Yan sanda sun kama mutumin da ake zargi da kwantawa da yar shekara 80 a Nasarawa
Yan sanda sun kama mutumin da ake zargi da kwantawa da yar shekara 80 a Nasarawa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Sanarwar ta ce an kai korafin lamarin ofishin yan sanda da ke Garaku a ranar 14 ga watan Janairu da misalin karfe 22:30pm, Daily Trust ta kuma rahoto.

An tattaro cewa wanda ake zargin mai suna Dan’asabe Eddo, ya kasance dan asalin jihar Kaduna amma mazaunin kauyen Kundami da ke Garaku, karamar hukumar Lokonga na jihar Nasarawa.

A cewar sanarwa:

"An yi zargin cewa ya shiga gidan tsohuwar mai shekara 80, wacce ke zama ita kadai a wannan kauyen, sannan ya kanta da ita ta karfi da yaji.
"Ana samun korafin, sai jami'an yan sandan Garaku suka shiga aiki sannan suka kama wanda ake zargin.
"A yayin amsa tambayoyi, wanda ake zargin ya bayyana cewa ya aikata laifin, amma ya dora alhakin hakan a kan sharrin shaidan.

Kara karanta wannan

Sarki a Arewa ya sha da ƙyar hannun matasa da suka kai hari fadarsa don ya gaza kare su daga harin ƴan bindiga

"Da aka sanar da shi, kwamishinan yan sandan jihar, CP Adesina Soyemi, ya yi umurnin mika lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar (SCID), Lafia, domin yin cikakken bincike."

Sanarwar ta bukaci jama’a da su mai da hankali sosai kan tsofaffi, tare da basu kariya.

A wani labari na daban, babban jagoran jam'iyyar All Progressive Congress (APC) na kasa, Bola Tinubu, ya ce Najeriya za ta yi nasara a yaki da fashi da makami, garkuwa da mutane, kashe-kashe da sauran matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu.

Tinubu ya bayar da tabbacin ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Janairu, lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari kan kashe kwamishinansa, Dr Rabe Nasir da aka yi a kwanan nan, rahoton PM News.

A cewarsa, kasar na da fadi kuma ta fi karfin wadannan miyagu, don haka ya kamata gwamnatin tarayya ta dauki dukkan matakai domin shafe su.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya karyata harin Boko Haram kan cibiyar horar da yan sanda a Gwoza

Asali: Legit.ng

Online view pixel