Yadda 'yan ta'adda suka bindige mutane 13 har lahira a harin Jihar Neja

Yadda 'yan ta'adda suka bindige mutane 13 har lahira a harin Jihar Neja

  • Ana ci gaba da samun bayanai dangane da yadda ‘yan bindiga suka shiga wasu garuruwa cikin karamar hukumar Shiroro da ke Jihar Neja
  • A ranar Talata suka kai farmaki Nakundna da Wurukuchi da ke karamar hukumar, sun halaka fiye da mutane 13 bayan sun ritsa su a gona
  • Harin ya auku ne duk da yadda jami’an tsaro suke ci gaba da sintiri a wasu garuruwa a Shiroro saboda ta’addancin da ke aukuwa

Neja - Ana samun bayanai akan yadda ‘yan bindiga suka kai farmaki wasu anguwanni da ke cikin karamar hukumar Shiroro a cikin jihar inda suka halaka fiye da mutane 13 a Nakundna da Wurukuchi ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.

Harin ya auku ne duk da yadda jami’an tsaro suke ci gaba da sintiri a wasu kauyaku da ke Shiroro da sauran kananun hukumomin da ta’addanci ya addaba a jihar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Akalla mutum 17 sun mutu, yayin da yan bindiga suka cinnawa gidaje wuta a Filato

Yadda 'yan bindiga suka bindige mutane 13 a harin Jihar Neja
'Yan bindiga sun harbe mutane 13 har lahira a harin Jihar Neja. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Harin ranar Talata ya auku ne bayan bai wuce makonni biyu ba da ‘yan bindiga suka kai wa ma’aikatan Zungeru Dam farmaki har suka halaka mutane biyu sannan suka yi garkuwa da wasu ‘yan China guda biyu.

Wasu mazauna yankin sun shaida wa wakilin Daily Trust cewa ba su samu damar kiran jami’an tsaro ba saboda an datse kafafen sadarwan yankin tun bayan harin da aka kai wa ma’aikatan Zungeru Dam.

‘Yan sanda sun hana mutane sanar da yawan wadanda hari ya shafa matsawar ba su tabbatar ba

Shugaban karamar hukumar Shiroro, Dauda Chukuba ya tabbatar da aukuwar harin inda ya ce ba su tabbatar da yawan wadanda suka cutu ba.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta ja kunne a kan jama’a su dinga karar da yawan wadanda rashin tsaro ya afka mawa ba tare da tabbatar da yawansu ba don gudun razanar da zuciyoyin jama’a.

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Wasiu Abiodun ya ce mutane 13 suka rasa rayukansu ba mutane 37 da jama’a suka dinga yadawa ba.

Har gona ‘yan bindigan suka bisu

A cewarsa, ‘yan bindigan da ake zargi sun kai wa ‘yan kauyen farmaki ne yayin da suke girbin shukokinsu a gonarsu da ke Nakundna kusa da Kaure a karamar hukumar Shiroro.

A cewarsa rundunar wacce kwamandan yankin Shiroro ya jagoranta ta je har inda lamarin ya auku.

Ya kara da cewa:

“Ba a samu bayanai akan yadda lamarin ya faru ba saboda rashin kafafen sadarwar da ke yankin.”

Gwamnan jihar ya yi alawadai da harin

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya kwatanta harin da ‘yan bindiga suka kai cikin karamar hukumar Shiroro a matsayin “rashin hankali” kuma ya ce ba za a lamunta ba.

Gwamnan ya saki wata takarda ta sakatariyar watsa labaransa, Mary Norl Berje, inda ya ce kisan na kauyanci da rashin imani ne.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kone kauyuka 5 kurmus, sun hallaka mutane a Zamfara

Gwamnan ya nuna matukar tausayawa ga wadanda lamarin ya shafa musamman mutanen Nakunda da Wurukuchi inda yace za a dauki matakai don hana hakan ya kara faruwa.

'Yan bindiga sun dira a Kano, sun sace mahaifiyar ɗan majalisa

A wani labarin, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, a ranar Laraba sun sace mahaifiyar Isyaku Ali-Danja, dan majalisa mai wakiltar mazabar Gezawa a majalisar jihar Kano.

Daily Nigerian ta rahoto cewa yan bindigan sun afka gidan mahaifiyar dan majalisar ne da ke Gezawa misalin karfe 1 na dare, suka balle kofa sannan suka yi awon gaba da ita.

Da ya ke bada labarin yadda abin ya faru, Mr Ali-Danja, wanda ya taba rike mukamin kakakin majalisa, ya ce da farko yan bindigan sun umurci mahaifiyarsa ta bude kofa amma ta ki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel