Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun dira a Kano, sun sace mahaifiyar ɗan majalisa

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun dira a Kano, sun sace mahaifiyar ɗan majalisa

  • Wasu miyagun yan bindigan da ba a san ko su wanene ba sun bi dare sun sace mahaifiyar Isyaku Ali-Danja, dan majalisar Jihar Kano
  • Ali-Danja, wanda ke wakiltar mazabar Gezawa ya magantu kan yadda 'yan bindigan suka nemi mahaifiyar ta bude kofa, ta ki budewa amma suka balle kofar suka sace ta
  • Ali-Danja ya ce kawo yanzu 'yan bindigan ba su tuntubi kowa ba game da batun fansa sannan an sanar da yan sanda sun fara bincike

Jihar Kano - Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, a ranar Laraba sun sace mahaifiyar Isyaku Ali-Danja, dan majalisa mai wakiltar mazabar Gezawa a majalisar jihar Kano.

Daily Nigerian ta rahoto cewa yan bindigan sun afka gidan mahaifiyar dan majalisar ne da ke Gezawa misalin karfe 1 na dare, suka balle kofa sannan suka yi awon gaba da ita.

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun dira a Kano, sun sace mahaifiyar ɗan majalisa
'Yan bindiga sun sace mahaifiyar dan majalisar Jihar Kano. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Mr Ali-Danja, dan majalsa mai wakiltar Gezawa ya tabbatar da afkuwar lamarin

Da ya ke bada labarin yadda abin ya faru, Mr Ali-Danja, wanda ya taba rike mukamin kakakin majalisa, ya ce da farko yan bindigan sun umurci mahaifiyarsa ta bude kofa amma ta ki.

Ya ce bayan ta ki bude kofar sai suka sa karfi suka balle kofar sannan suka sace ta.

Mr Ali-Danja ya kara da cewa nan take bayan maharan sun bar gidan, daya daga cikin masu kula da dattijuwar ta sanar da su abin da ya faru, aka kuma sanar da yan sanda nan take, rahoton Daily Nigerian.

Dan majalisar ya ce:

"Tun kafin in tafi Gezawa, DPO na yan sandan yankin ya kira ni ya ce sun tura jami'ansu wurin da abin ya faru. Ya ce tuni sun fara bincike kan lamarin."

Mr Ali-Danja ya kuma ce kawo yanzu yan bindigan ba su tuntube shi ba ko wani daga cikin yan uwansa game da biyan kudin fansa.

Ya kara da cewa:

"Har yanzu ba su tuntubi kowa ba. Muna dai addu'ar Allah ya tseratar da ita."

Yadda jami'an DSS 5 suka taimaka min na yi garkuwa da kwastoma na, Wanda ake Zargi

A wani labarin, kun ji cewa wani Akeem Ogunnubi mai shekaru 42 ya bayyana yadda ya yi garkuwa da wani dan kasuwa a Sabo mai suna Bola cikin ranakun karshen mako, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olawale Olokode dama ya bayar da labari yayin tasa keyar mutumin da ake zargi cewa wasu maza dauke da bindigogi sun sace wani dan canji har cikin ofishinsa a ranar 30 ga watan Disamban 2021 da misalin karfe 5:30 da yamma.

Wanda lamarin ya faru da shi kamar yadda Olukode ya shaida ya ce sun zarce da shi daji ne sannan suka bukaci kudin fansa kafin su sake shi, a nan su ka yi masa kwacen N204,000 sannan suka tsere suka bar shi a wurin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel