Innalillahi: 'Yan bindiga sun kone kauyuka 5 kurmus, sun hallaka mutane a Zamfara

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kone kauyuka 5 kurmus, sun hallaka mutane a Zamfara

  • Miyagun 'yan bindiga sun sake kai mummunan hari wasu yankunan jihar Zamfara, sun hallaka mutane da dama
  • Hakazalika, sun kone kauyuka biyar kurmus, lamarin da ya raba mutane da dama da gidajensu a kauyukan
  • A halin yanzu dai suna ta tururuwa zuwa garin Anka domin tsira da rayukansu da sauran abin da ya rage musu

Zamfara - Daruruwan mazauna kauyuka biyar ne a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum na jihar Zamfara suke ta tururuwa zuwa cikin garin Anka bayan da ‘yan bindiga suka kashe mutane da dama a kauyukansu.

Majiyoyi da suka zanta da jaridar Premium Times sun ce har yanzu ba a tantance adadin wadanda aka kashe ba.

Mazauna Zamfara sun shiga tasku saboda 'yan bindiga
Innalillahi: 'Yan bindiga sun kone kauyuka 5 kurmus, sun hallaka mutane a Zamfara | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani lauya wanda kuma mamba ne a kungiyar agaji ta Zamfara, ya ce ya ga yawancin mutanen kauyen da suka rasa matsugunai a sakateriyar karamar hukumar Anka.

Kara karanta wannan

Maimakon mika wa 'yan sanda, 'yan banga sun hallaka 'yan leken asirin 'yan bindiga a Zamfara

Majiyar da ta nemi a sakaya sunanta ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kafin na tafi Gusau a safiyar yau na kirga sama da mutane 500, yawancinsu tsoffin mata da mata da yara. An fara kai harin ne daga daren ranar Talata zuwa Laraba.”

Ya ce ma’aikatan sa kai na gida bisa umarnin Sarkin Zamfara Anka suna tallafa wa ‘yan gudun hijirar.

Kauyukan da aka kai wa hari

Premium Times ta tattaro cewa kauyukan da aka kai harin sun hada da Tungar Geza, Rafin Gero, Kurfar Danya, Kewaye da Tungar Na More.

Wata majiya da ta zanta da Sashen Hausa na Muryar Amurka ta ce an fara kai hare-haren ne daga Barikin Daji a wani harin da aka bayyana a matsayin fada tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan Sakai.

A cewar majiyar:

“Sun yi ta fafatawa tun jiya (daren Talata). Abin da ya ba mu tsoro shi ne yadda suka yi nasarar raba Kurfar Danya. Kun san an ce ba a iya shiga Kurfar Danya, amma na rantse da Allah (’yan bindiga) sun kona garin kurmus.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun bude wa mutane wuta a Zariya, sun kashe mutane

“Sun koma zuwa Tungar Na More da Rafin Gero. Kamar yadda nake magana da ku yanzu, wasu gidaje na ci gaba da cin wuta a Rafin Gero. Tungar Isa da Barayar Zaki su ma wasu kauyuka ne da aka kona.”

Yayin da ya kasa tabbatar da adadin wadanda aka kashe, majiyar ta ce mutane da dama da suka tsira zuwa garin Anka ba su iya gano danginsu ba.

Shugaban matasa a karamar hukumar Bukkuyum, Abubakar Gero, ya tabbatar da cewa an fara kai hare-haren ne a Kurfar Danya.

A cewar Abubakar Gero:

“Hare-haren suna da alaka. ’Yan bindigan sun fara kai wa al’umma hari daga Bukkuyum. Mun tattaro cewa sun zo daruruwansu ne saboda mutanen kauyen suna tinkarar duk wani yunkurin kai hari a kauyensu.
“Bayan sun kai hari Kurfar Danya sun kuma kai hari Ruwan Jema suka kashe da dama tare da kona kayan abinci kurmus. Ina mai tabbatarwa da safiyar yau sun koma Ruwan Jema. Har yanzu jama'ar yankin ba su tantance matakin barnar ba saboda har yanzu suna kan gudu."

Kara karanta wannan

Ku yiwa 'yayanku tarbiyya bisa al'adunmu, Lai Mohammed ya yi kira ga iyaye

Ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun ‘yan sanda a Zamfara, Mohammed Shehu kasancewar layin wayarsa ba ya shiga.

Wannan mummunan harin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kokarin dakile ayyukan ta'addanci a yankin Arewa maso yammaci da gabashin kasar nan.

Wasu bakin mutane akalla 600 sun shiga wata jiha a Arewa a Tirela biyu

A wani labarin, matasan garin Maihula dakekƙaramar hukumar Bali a jihar Taraba sun kori waru bakin mutane akalla 600, waɗan da suka shiga garin a cikin Tirela guda biyu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa baƙin waɗan da suka haɗa da; mata da kananan yara, ana tsammanin daga jihar Zamfara suka fito.

Wani mazaunin garin Maihula, Mallam Yakubu Bello, ya shaida wa manema labarai cewa, sun gano bakin da suka shigo garin ne da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel