Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai sabon mummunan hari jihar Filato, sun kashe mutane da kona gidaje

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai sabon mummunan hari jihar Filato, sun kashe mutane da kona gidaje

  • Wani sabon hari da yan bindiga suka kai jihar Filato ya lakume rayukan mutane da basu ji ba kuma ba su gani ba akalla 17
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun shiga kauyen Ancha da dare, suka bude wa mutane wuta kuma suka cinnawa gidaje wuta
  • Gwamna Simong Lalong, ya umarci hukumomin tsaro su damƙo masu hannu a harin ta kowane hali

Plateau - Akalla mutum 17 aka tabbatar sun mutu, yayin da gidaje da yawa suka ƙone a wani sabon mummunan hari da yan bindiga suka kai yankin Ancha dake Bassa, a jihar Filato.

The Nation ta ruwaito cewa maharan sun farmaki yankunan da adadi mai yawa na mayaƙa, suka bude wa mutane wuta kan mai uwa da wabi.

Yan bindigan da ake zaton fulani makiyaya ne, sun kashe mutane kuma suka cinna wa gidaje wuta, tare da tilasta wa wasu tserewa domin ceton rai.

Kara karanta wannan

Watanni bayan mutuwar wani Mufti, Kyanwarsa taki tashi daga kan kabarinsa

Yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai sabon mummunan hari jihar Filato, sun kashe mutane da kona gidaje Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar soji ta Operation Safe Haven, Manjo Ishaku Takwa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Da daren ranar Talata, 11 ga watan Janairu, mun samu kiran gaggawa na kai hari ƙauyen Ancha dake karamar hukumar Bassa, a jihar Filato."
"Nan take dakarun Operation Safe Haven suka shirya suka nufi ƙauyen. Lokacin da suka isa maharan sun tsere, sun kona gidaje kuma mazauna kauyen da dama sun mutu."
"Sojoji na cigaba da bibiyar maharan, zamu sanar da zaran an samu cigaba. Kwamandan sojojin ya jajantawa iyalan mamatan, kuma ya tabbatar da cewa waɗan da suka aikata haka zasu girbi abin da suka shuka."

Lalong ya nuna rashin jin dadinsa

Gwamnan jihar, Simon Lalong, ya bayyana matuƙar damuwarsa kan harin duk da matakan da gwamnatinsa ta ɗauka.

Ya kuma umarci hukumomin tsaro su tabbata sun kame duk masu hannu a lamarin ta kowane hali, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan daba sun wanke jigon APC da wasu mutane da ruwan 'Acid' a Adamawa

A wata sanarwa da kakakinsa, Makut Simon Macham ya fitar, Lalong ya roki shugabannin tsaro dake jihar su yi amfani da bayanan waɗan da suka tsira daga harin wajen binciko yan ta'addan.

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta bayyana mutanen da take zargin suna da hannu a ta'addancin yan bindiga

PDP ta yi kira da babban murya ga hukumomin tsaro su kira shugabannin APC mai mulki domin amsa tambayoyi kan alaƙa da yan ta'adda.

PDP tace bai kamata jami'an tsaro su kyale ikirarin da tsohon jigon APC ya yi ba kan shigo da yan ta'adda Najeriya a 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel