Yadda jami'an DSS 5 suka taimaka min na yi garkuwa da kwastoma na, Wanda ake Zargi

Yadda jami'an DSS 5 suka taimaka min na yi garkuwa da kwastoma na, Wanda ake Zargi

  • Wani Akeem Ogunnibi mai shekaru 42 ya bayyana yadda ya yi garkuwa da wani dan kasuwa a Sabo mai suna Bola da taimakon jami’an DSS 5
  • Kwamishinan ‘yan sanda, Olawale Olokode ya bayyana yadda wani wasu maza rike da bindiga su ka sace wani dan canji daga ofishinsa da ke Osogbo ranar 30 ga watan Disamban 2021
  • Kamar yadda Olokobe ya shaida, sun wuce da shi wani daji ne da ke kan titin Ilesa sannan su ka kwace masa N204,000 da ke tare da shi su ka tsere

Jihar Osun - Wani Akeem Ogunnubi mai shekaru 42 ya bayyana yadda ya yi garkuwa da wani dan kasuwa a Sabo mai suna Bola cikin ranakun karshen mako, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olawale Olokode dama ya bayar da labari yayin tasa keyar mutumin da ake zargi cewa wasu maza dauke da bindigogi sun sace wani dan canji har cikin ofishinsa a ranar 30 ga watan Disamban 2021 da misalin karfe 5:30 da yamma.

Yadda jami'an DSS 5 suka taimaka min na yi garkuwa da kwastoma na, Wanda ake Zargi
Wani da ake zargi ya ce jami'an DSS 5 suka taimaka masa ya yi garkuwa da kwastomansa. Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wanda lamarin ya faru da shi kamar yadda Olukode ya shaida ya ce sun zarce da shi daji ne sannan suka bukaci kudin fansa kafin su sake shi, a nan su ka yi masa kwacen N204,000 sannan suka tsere suka bar shi a wurin.

Vanguard ta rahoto yadda Ogunnibi ya ce ya hada kai da wasu jami’an DSS wurin yin garkuwa da dan kasuwar.

A cikin 210,000 da jami’an su ka amsa, N15,000 kacal su ka ba shi

Kamar yadda yace:

“Bala, (wanda ibtila’in ya fada masa) abokina ne, ya biya wani bangare na kudin wata sarkar zinari wacce ya siya a hannun ‘yan uwana, lokacin da na same shi, ban gamsu da bayanansa ba hakan ya sa na kira masa jami’an DSS don su ladabtar min da shi.

“Ya biya N680,000 a matsayin kudin sarka mai kimar N972,000 don haka na kira jami’an DSS 5 muka je har wurin aikinsa sannan muka wuce ofishinsu da ke Osogbo.”

An kama jami’an

Ya kara da cewa an kama jami’an DSS din, don ya gani da idanunsa.

Kamar yadda ya shaida:

“Ba a shigar da shi cikin Ofishin ba, sai su ka amshi kudi a hannunsa, ina cikin motar da su ka yi ciniki da shi, amma ya biya su N210,000 ni kuma su ka ba ni N15,000.
“An kama jami’an DSS din amma ban san meyasa ba a tasa keyarsu ba don tabbas an kama su.”

Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da cewa ana ta kokarin kawo sauran wadanda ake zargin don su amsa tambayoyi.

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.

An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Yan sandan suna zarginsa da:

"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".

Asali: Legit.ng

Online view pixel