Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

  • Jami'an yan sandan Jihar Katsina sun yi nasarar cafke wani Usama Tijjani da ake zargi da yaudarar yan mata ta hanyar intanet
  • Tijjani ya kware ni wurin jan hankalin mata ta soshiyal midiya, sannan ya gayyace su otel, ya kwana da su amma sai sace musu waya, kudi da sauransu ya tsere.
  • Asirinsa ya tonu ne bayan ya gayyaci wata yarinyar yar asalin Jihar Katsina zuwa Kano ya mata alkawarin zai biya ta N50,000 amma ya tsere lokacin tana wanka

Jihar Katsina - Jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.

An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Kara karanta wannan

Nasrun minallah: Yan sanda sun bindige yan bindiga 38 har lahira a jihar Katsina

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi
Katsina: An cafke wani da ke yaudarar mata ta intanet ya gayyace su otel, ya kwana da su sannan ya musu sata. Hoto: Vanguard.
Asali: Facebook

Yan sandan suna zarginsa da:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci."

Mai magana da yawun yan sanda, SP Gambo Isah, wanda ya yi holen Tijanni a gaban manema labarai ya ce an dauki mataki a kansu ne bayan yan matan Katsina da dama sun shigar da korafi a kansa.

"Bayan samun korafi daga mata da dama a birnin Katsina da ke cewa wanda ake zargin ya kware wurin yaudarar yan sanda a soshiyal midiya ta hanyar gayyatarsu otel a jihohi daban-daban, ya kwanta da su sannan ya sace wayoyinsu, kudinsu da sauran kayayyaki masu muhimmanci.
"Asirinsa ya tonu ne bayan ya gayyaci wata yarinya yar asalin jihar Katsina zuwa otel a Kano, ya yi alkawarin zai biya ta N50,000, amma bayan ya kwana da ita, ya tsere daga otel din da safe yayin da ta ke wanka."

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Gwarazan yan sanda sun damke kasurgumin dan bindiga da ya addabi Zamfara

Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel