Ikon Allah: Yadda raken N50 ya jawo rikicin da ya kai ga zub da jini da garkame kasuwa a jihar Kwara

Ikon Allah: Yadda raken N50 ya jawo rikicin da ya kai ga zub da jini da garkame kasuwa a jihar Kwara

  • Rake ya haddasa gagarumin rikici wanda ya har sai da ya kai ga zubar jini a wata kasuwa a garin Ilorin
  • Rikicin ya fara ne lokacin da wani mutum ya siyi raken N50 amma sai ya ji shi salam babu zaki inda ya nemi mai siyarwan ya sauya masa wani
  • Ana haka mai raken ya ce ba zai canja ba inda daga bisani ya soki mutumin, nan take sai lamarin ya kazanta

Kwara - An samu tashin hankali a sananniyar kasuwar nan ta Mandate da ke garin Ilorin, jihar Kwara a ranar Talata, 4 ga watan Janairu, tsakanin wani mai saida rake da mai siya kan raken naira 50.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya zama na mutane da yawa yayin da bangarorin da ke adawa suka yi amfani da makamai.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Yadda uwa ta haifi jariri a cikin jirgin sama ta jefar dashi bandakin jirgi

Rikicin ya yi sanadiyar rufe kasuwar na tsawon awanni masu yawa.

Ikon Allah: Yadda raken N50 ya jawo rikicin da ya kai ga zub da jini da garkame kasuwa a jihar Kwara
Ikon Allah: Yadda raken N50 ya jawo rikicin da ya kai ga zub da jini da garkame kasuwa a jihar Kwara Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: Facebook

An kuma tattaro cewa an gaggauta kwasar wasu mutane da suka jikkata sakamakon soke-soke da aka yi zuwa wani babban asibiti mafi kusa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma wata majiya ta ce wasu tsageru da suka saba yawo a kasuwar ne suka fara fada da wani lamarin da ya kai ga barkewar rikicin.

Harkokin kasuwanci sun tsaya cak yayin da rikicin ya shafe tsawon lokaci inda jami'an 'yan sanda suka isa wajen domin ganin an dawo da zaman lafiya a kasuwar.

‘Yan kasuwan a kasuwar, sun nuna fargaba kan yiwuwar kai wani harin idan har ba a magance matsalar ba.

A rahoton Daily Post, an zuba jami'an tsaro a mashigin wajen domin hana ci gaban karya doka da oda.

Yadda rigimar ta fara

Da yake magana kan ci gaban, kakakin rundunar NSCDC, Babawale Afolabi, ya ce rikicin ya fara ne lokacin da wani mutum ya siya raken N50 amma ya ga cewa babu zaki.

Kara karanta wannan

Bidiyon matasan da suka shiga hannu yayin da suke kokarin yin asirin kudi da wata budurwa

Ya ce mutumin ya nemi mai raken ya canja masa amma sai ya ki inda daga bisani ya soki mai siyan da wuka.

Bidiyon matasan da suka shiga hannu yayin da suke kokarin yin asirin kudi da wata budurwa

A wani labari na daban, mun ji cewa wata matashiyar budurwa mai shekaru 14 ta tsallake rijiya da baya a ranar Litinin, 3 ga watan Janairu, lokacin da wasu matasa biyu suka yi kokarin yin asirin kudi da ita a jihar Bayelsa.

Jama'a sun damke matasan biyu masu shekaru 16 a safiyar Litinin, a garin Sagbama da ke karamar hukumar Sagbama na jihar.

An tattaro cewa matasan sun yaudari yarinyar da kullin asirinsu zuwa wani kango domin aiwatar da mugun nufinsu, amma sai suka taki rashin sa'a yayin da wani mai wucewa ya hangesu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel