Dubu ta cika: Wani mutumi ya yi lalata da mata 10 a Otal da sunan Kwamishinan jiha

Dubu ta cika: Wani mutumi ya yi lalata da mata 10 a Otal da sunan Kwamishinan jiha

  • Yan sanda sun yi ram da wani mutumi bisa zargin amfani da sunan kwamishinan Akwa Ibom yana damfaran mutane
  • Kakakin yan sanda na jihar, Odiko Macdon, yace wanda ake zargi ya kwanta da mata 10 bisa alkawarin zai taimaka musu su samu aiki
  • Mutumin mai suna Imaobong Akpan, ya amsa laifinsa tare da bayyana irin ta'asar da ya yi da sunan kwamishinan

Akwa Ibom - Jami'an yan sanda reshen jihar Akwa Ibom na sashin yaƙi da manyan laifuka, sun cafke wani dan damfara, Imaobong Akpan, bisa zargin yin sojan gona da kwamishinan ƙasa da albarkatun ruwa na jihar.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Odiko MacDon, shine ya bayyana haka yayin da yake shigar da wanda ake zargi hedkwatar yan sanda ranar Talata.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun bude wa mutane wuta a Zariya, sun kashe mutane

Punch ta rahoto cewa wanda ake zargin ya shiga hannun jami'an yan sanda ne bayan samun korafe-korafe kan abin da yake aikatawa.

Yan sanda
Dubu ta cika: Wani mutumi ya yi lalata da mata 10 a Otal da sunan Kwamishinan jiha Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Haka nan kuma ya bayyana abubuwan da aka samu a hannun mutumin da suka haɗa da, layukan waya 5, wayoyin hannu biyu da kuma dalar Maurka 5, da kudin China 7.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin ya yaudari mata 10

MacDon ya ƙara da cewa mutumin da ake zargin, bayan yin badda kama da sunan kwamishina a Facebook, ya kuma damfari mutane da dama.

A cewarsa mafi yawancin waɗan da ya damfara mata ne, inda yake samar musu aiki na ƙarya bayan ya yi lalata da su, kamar yadda Linda Ikeji ta rahoto.

Kakakin yan sandan yace:

"Mutumin da ake zargin sanannen ɗan damfara ne da neman mata, ya amince da cewa ya kirkiri shafin Facebook na damfara."

Kara karanta wannan

Gaskiyar yadda muka kubuta daga hannun kasurgumin dan bindiga Turji, Ibrahim ya magantu

"Ya yi amfani da wannan shafin wajen yaudarar mata zuwa Otal, ya kwanta da su bisa alƙawarin zai taimaka musu su samu aiki, yayin da ya damfari mutane kuɗaɗe miliyoyi."
"Ya samu nasarar yaudaran mata 10 da wannan shafin na Facebook kuma ya kwanta da su a Otal daban-daban, yayin da yake nuna musu shi mai taimaka wa kwamishina ne na musamman."

A wani labarin kuma Matan Arewa sun bayyana sunan gwamnan da suke kaunar ya gaji Buhari a zaben 2023

Kungiyar matan Arewa sun tabbatar wa gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi goyon bayan su a babban zaben 2023.

Matan karkashin kungiyar YBN sun bayyana cewa gwamna Bello ya nuna zai iya jagorancin Najeriya duba da nasarorinsa a Kogi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel