Gombe: Mai adaidaita sahu ya yi garkuwa da kansa don ya samu N500,000 ya biya bashin da 'yar uwarsa ke binsa

Gombe: Mai adaidaita sahu ya yi garkuwa da kansa don ya samu N500,000 ya biya bashin da 'yar uwarsa ke binsa

  • Yan sanda sun yi nasarar kama wani mutum, Halilu Aliyu, da abokinsa Ahmed Ladan kan zarginsu da kitsa garkuwa da mutum na karya
  • Aliyu dai ya yi garkuwa da kansa ne da nufin ya tatsi kudi N500,000 daga hannun yayansa Zainab Aliyu ya biya kudin adaidaita sahu da ya sayar ya cinye
  • Wata 'yar uwan Aliyu ne ta bashi adaidaita sahu ya rika aiki bayan kasuwancinsa ya rushe amma ya sayar ba tare da saninta ba hakan tasa ya shirya garkuwar da kansa don ya biya ta

Gombe - Jami'an yan sanda a jihar Gombe sun kama wani Halilu Aliyu, mai adaidaita sahu, saboda yin karyar cewa an yi garkuwa da shi saboda bashin N250,000 da ake binsa, The Punch ta ruwaito.

Ita ma The Cable ta ruwaito cewa an kama Aliyu, mai shekaru 32, tare da Ahmed Ladan, mai shekaru 42, wanda ake zargi tare suka kitsa makircin.

Kara karanta wannan

Ina fatan na sake ganinsa: Inji attajirin mahaifin Abdul Mutallab, wanda aka kama da bam a Amurka

Gombe: Mai adaidaita sahu ya yi garkuwa da kansa don ya samu N500,000 ya biya bashi
Mai keke napep ya kitsa garkuwa da kansa don ya samu N500,000 ya biya bashin da 'yaruwarsa ke binsa. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Yan sandan sun ce wanda ake zargin ya fada matsala ne bayan ya sayar da keke napep din da yar uwarsa ta bashi domin ya yi kasuwanci.

An ce Aliyu ya bullo da wannan shirin ne domin ya samu kudin da zai biya 'yar uwarsa kudinta duba da cewa tana tambayan inda keke napep dinta ya ke.

Mary Malum, mai magana da yawun yan sandan Gombe ta ce:

"Yar uwarsa ne ta bawa wanda ake zargin na farko, Haliru Aliyu, namiji, mazaunin Tudun Wada quarters a Gombe adaidaita sahu bayan kasuwancinsa ya rushe."
"Amma daga bisani, wanda ake zargin ya sayar da adaidaita sahun ba tare da sanin mai shi ba a kan N250,000.
"Da mai keken ta tambaya keken ta ko kudi, wanda ake zargin ya gaza biya.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Yadda raken N50 ya jawo rikicin da ya kai ga zub da jini da garkame kasuwa a jihar Kwara

"Saboda kunya a cewarsa, a ranar 30 ga watan Disambar 2021, wanda ake zargin ya tafi gidan abokinsa, wanda ake zargi na biyu, wani Ahmed Ladan, inda suka kitsa garkuwa na karya domin su amshi kudi hannun yayansa Zainab Aliyu, kudi N500,000 don ya samu ya biya bashin."

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.

An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Yan sandan suna zarginsa da:

"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".

Kara karanta wannan

Bidiyon matasan da suka shiga hannu yayin da suke kokarin yin asirin kudi da wata budurwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel