'Yan bindiga sun kai wa fasinjoji hari a jirgin ruwa, sun yi musu fashi sun kuma sace jirgin

'Yan bindiga sun kai wa fasinjoji hari a jirgin ruwa, sun yi musu fashi sun kuma sace jirgin

  • Wasu bata garin yan bindiga sun kai wa wani jirgin ruwa da ke dauke da fasinjoji hari a Twon Brass a jihar Bayelsa
  • Yan bindigan sun yi wa mutanen da ke jirgin ruwan fashi sannan suka sauke su tare da direba jirgin a daji suka yi awon gaba da jirgin
  • Shugaban Kungiyar Ma'aikatan Jiragen Ruwa ta Najeriya, Mr Ogoniba Ipigansi ya tabbatar da afkuwar lamarin a Yenagoa

Jihar Bayelsa - 'Yan bindiga sun afka wa wani jirgin kasa mai dauke da fasinjoji a ranar jejiberin sabuwar shekara a Bayelsa, Daily Trust ta ruwaito.

Jirgin mai dauke da fasinjoji 14 ya bar Yenagoa yana hanyarsa na zuwa karamar hukumar Twon Brass a yayin da yan bindigan suka kai musu hari, kamar yadda kamfanin dillancin Najeriya, NAN, ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun tarwatsa shugabannin 'yan bindiga a Zamfara

'Yan bindiga sun kai wa fasinjoji hari a jirgin ruwa, sun yi musu fashi sun kuma sace jirgin
'Yan bindiga sun afka wa fasinjoji a jirgin ruwa, sun musu fashi a Bayelsa. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun tsere da injin mai karfin horsepower 115 kirar Yamaha da ke jirgin ruwan sannan suka kwace wa fasinjojin dukkan abubuwa masu muhimmanci da suke dauke da su, rahoton Daily Trust.

Shugaban Kungiyar Ma'aikatan Jiragen Ruwa ta Najeriya, Mr Ogoniba Ipigansi ya shaidawa NAN a Yenagoa a ranar Lahadi cewa babu fasinja ko daya da aka yi wa rauni.

Ya ce:

"Yan bindigan sun yi watsi da direban jirgin da fasinjojin a daji kafin suka yi awon gaba da injin."

Ipigansi kuma ya ce an tura jami'an tsaro zuwa wurin da suka faru domin ceto wadanda abin ya shafa.

'Yan bindiga sun afka cibiyar lafiya, sun kashe dan sanda sun kuma sace wani dan sandan

A wani labarin, 'yan bindiga sun kai farmaki asibitin Eziama-Uli da ke karamar hukumar Ihiala da ke jihar inda suka halaka wani dan sanda sannan su ka yi garkuwa da daya, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hatsarin kwale-kwale: Fasto da wasu mutane shida sun mutu a jajiberin sabuwar shekara

Lamarin ya auku ne a daren Laraba yayin da ake wani shirin kiwon lafiya wanda Uli Global Ambassadors for Development Initiative ta shirya don al’umma.

Ganau sun bayyana yadda lamarin ya faru a ranar Alhamis inda ya ce ‘yan bindiga sun afka wurin da ake shirin, su ka dinga harbe-harbe ko ta ina wanda hakan ya janyo masu shirin da sauran jama’a su ka dinga tserewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel