Hatsarin kwale-kwale: Fasto da wasu mutane shida sun mutu a jajiberin sabuwar shekara

Hatsarin kwale-kwale: Fasto da wasu mutane shida sun mutu a jajiberin sabuwar shekara

  • Wani abun bakin ciki ya cika da l'umman garin Ogbinbiri da ke karamar hukumar Ijaw ta kudu a jihar Bayelsa sun shiga alhini a jajiberin sabuwar shekara
  • Babban faston garin da wasu mutane shida sun rasa ransu a hatsarin kwale-kwale da ya afku a ranar Juma'a, 31 ga watan Disamba
  • Lamarin ya wakana ne lokacin da wasu kwale-kwale biyu suka kara a hanyarsu ta kai wata mara lafiya Yenagoa domin jinya

Bayelsa - Al'umman garin Ogbinbiri da ke karamar hukumar Ijaw ta kudu a jihar Bayelsa sun shiga alhini a jajiberin sabuwar shekara sakamakon mutuwar wani fasto da wasu mutane shida.

A cewar idon shaida, lamarin ya afku ne lokacin da wasu kwale-kwale biyu suka yi karo, inda suka kife a ranar Laraba, 31 ga watan Disamba.

Marigayin mai shekaru 39 wanda aka ambata da suna Fasto Salvation Degemy, ya kasance shugaban cocin Supernatural Church of God da ke garin, jaridar The Sun ta rahoto.

Hatsarin kwale-kwale: Fasto da wasu mutane shida sun mutu a jajiberin sabuwar shekara
Hatsarin kwale-kwale: Fasto da wasu mutane shida sun mutu a jajiberin sabuwar shekara Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Sauran mutanen da abun ya ritsa da su sun hada da wani magidanci, matarsa mara lafiya, yaransu biyu da kuma sauran dangi da ke a hanyarsu ta zuwa Yenagoa daga garin.

Majiyoyi sun ce daya daga cikin kwale-kwalen wanda a ciki ne iyalan da faston ke tafiya yana dauke da wata mara lafiya zuwa Yenagoa domin samun kulawar gaggawa lokacin da abun ya faru.

A cewar majiyoyin, an fara kwantar da mara lafiyar a asibitin Cottage da ke garin amma sai aka yanke shawarar mayar da ita Yenagoa saboda karancin na'urar shakar iska a asibitin, rahoton Nigerian Tribune.

Majiyar ta ce:

"An bayar da shawarar daukarta zuwa cibiyar kiwon lafiya ta tarayya da ke Yenagoa don samun na'urar shakar iskar. Suna a hanyarsu ta zuwa wajen ne lokacin da hatsarin ya afku.

"Fasto Salvation Degemy ya bisu ne domin yiwa mara lafiyar addu'a."

Majiyoyi sun ce mummunan al'amarin ya kawo cikas ga bikin sabuwar shekara a garin domin mutane da dama na cikin halin juyayi.

Hatsarin jirgin ruwa ya halaka magidanci, matansa biyu da dansa a Neja

A wani labarin, mun kawo a baya cewa a kalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a kauyen Zhigiri a karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai wani magidanci mai suna Mallam Mu'azu Babangida, matansa biyu da kuma babban dansa.

Kakakin gamayyar kungiyar Shiroro, Salis Mohamed Sabo, ya fada ma jaridar cewa lamarin ya afku ne lokacin da mazauna kauyen suke hanyarsu ta zuwa Dnaweto, wani kauye da ke makwabtaka domin halartan taron suna da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel