'Yan bindiga sun afka cibiyar lafiya, sun kashe dan sanda sun kuma sace wani dan sandan

'Yan bindiga sun afka cibiyar lafiya, sun kashe dan sanda sun kuma sace wani dan sandan

  • ‘Yan bindiga sun kai farmaki asibitin Eziama-Uli da ke karamar hukumar Ihiala da ke jihar Anambra inda su ka halaka wani dan sanda sannan su ka yi garkuwa da daya
  • Lamarin ya auku ne a daren Laraba yayin da ake wani shirin kiwon lafiya da Uli Global Ambassadors for Development Initiative ta shirya don al’umma
  • Ganau sun bayyana yadda lamarin ya auku inda ‘yan bindigan su ka kai farmaki ana tsaka da shirin su na harbe-harbe take anan jama’a su ka watse

Anambra - ‘Yan bindiga sun kai farmaki asibitin Eziama-Uli da ke karamar hukumar Ihiala da ke jihar inda suka halaka wani dan sanda sannan su ka yi garkuwa da daya, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kasa da sa'o'i 10 da aure, ango ya masgi amarya, ta tsere ta bar shi tare da kashe auren

Lamarin ya auku ne a daren Laraba yayin da ake wani shirin kiwon lafiya wanda Uli Global Ambassadors for Development Initiative ta shirya don al’umma.

'Yan bindiga sun afka cibiyar lafiya, sun kashe dan sanda sun kuma sace wani dan sandan
Yan sanda sun kai hari a cibiyar lafiya a Anambar, sun halaka dan sanda daya sun sace daya. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ganau sun bayyana yadda lamarin ya faru a ranar Alhamis inda ya ce ‘yan bindiga sun afka wurin da ake shirin, su ka dinga harbe-harbe ko ta ina wanda hakan ya janyo masu shirin da sauran jama’a su ka dinga tserewa.

Babu wanda ya san dalilin farmakin

Babu wanda ya san abinda ya janyo farmakin. The Punch ta gano yadda mutane da dama ciki har da marasa lafiya su ka samu raunuka yayin tserewa daga maharan.

A cewar ganau din, wanda ya ki bayyana sunansa, ‘yan bindigan sun yi garkuwa da wani dan sanda.

Kamar yadda ya shaida:

“Yan bindigan sun harbe ‘yan sanda biyu, daya ya mutu take a wurin, dayan kuma ya raunana, hakan ya sa aka wuce da shi asibiti don a kula da shi. Na ukun kuma sun tsere da shi, har yanzu ba a san inda yake ba.”

Kara karanta wannan

Yadda ɗan gani kashenin Buhari ya koma Kwankwasiyya bayan ƴan bindiga sun sace ƴan uwansa 5

Wani ma’aikacin ULIGADI, wanda ya ki sanar da sunansa sakamakon rashin samun izinin magana, ya tabbatar da harin.

Dayan yana asibiti ana kulawa da shi

Kamar yadda yace:

“Wani dan sanda ya mutu sakamakon harin. Dayan dan sandan kuma yana asibiti ana kulawa da lafiyarsa. Yanzu muna neman dayan dan sandan ne. Masu bincike su na kokarin ceto shi.”

Dan sandan da ya rasa ransa sunansa Sifeta Ezekiel Aliyu, ba a tabbatar da sunan dayan wanda ya ji raunin ba amma yana asibiti.

‘Yan sandan ma’aikatan 19 Police Mobile Force ne.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya tabbatar da harin

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Mr Ikenga Tochukwu, yace yanzu haka rundunar ‘yan sandan ta na kokarin gano maharan.

A cewarsa lamarin da ya faru a Eziama Uli yana nuna sadaukarwa irin ta jami’an ‘yan sanda ne ga kasa da kuma al’umma.

Ya ce har yanzu ‘yan sanda su na bincike akan yadda lamarin ya auku. Kuma za su saki bayanai idan sun kammala binciken.

Asali: Legit.ng

Online view pixel