Nasara daga Allah: Sojoji sun tarwatsa shugabannin 'yan bindiga a Zamfara

Nasara daga Allah: Sojoji sun tarwatsa shugabannin 'yan bindiga a Zamfara

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar ragargazar mafakar 'yan bindiga a wani yankin jihar Zamfara
  • Jihar Zamfara na fama da yawaitar 'yan ta'adda, inda aka hallaka mutane tare da sace wasu da dama a shekarun nan
  • An samu nasarar hallaka wasu manyan shugabannin 'yan bindiga; Alhaji Auta da wani kasurgumi Kachalla Ruga

Zamfara - Wasu 'yan bindiga da suka yi kaurin suna a yankunan jihar Zamfara, Alhaji Auta da Kachalla Ruga, sun halaka a wani harin da sojojin saman Najeriya suka kai ta sama.

An kuma hallaka da dama daga cikin ’yan tawagarsu a yayin farmakin da suka kai wa sansaninsu da ke Jama’are Bayan Dutchi, a gundumar Nasarawa Mailayi a Jihar Zamfara, a ranar Asabar.

Dan bindiga ya tarwatse a harin soji
Da Duminsa: Kasurgumin Dan bindigan da ya addabi Zamfara ya tarwatse | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Majiyoyi da dama sun tabbatar wa jaridar Daily Trust rasuwar Auta amma sun ce ba a san adadin wadanda suka mutu a harin ba.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun kai samame sansanin ‘yan bindiga a Kaduna, sun ceto mutum 9

Auta na cikin kasurgumai hudu na ‘yan bindigar da ke ta’addanci a yankin.

A rahoton da PR Nigeria ta ruwaito, ta ce a harin na sojoji an kuma kashe shugaban 'yan bindiga Kachalla Ruga.

Wani jami’in leken asiri na soji ya shaida cewa biyo bayan harin da jiragen yakin NAF suka kai kan ‘yan bindigan da suke shirin tserewa da kuma wadanda suka fake a karkashin bishiyu a yankin, ya yi sanadin salwantar rayuka da dama daga bangaren 'yan ta'addan.

Sojoji sun ragargaji 'yan ISWAP a Yobe, sun kama da dama sun hallaka 7

A wani labarin, a ranar Lahadi, 26 ga watan Disamba ne mayakan ISWAP suka kaddamar da hari a garin Buni Yadi dake karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe, amma sojojin Najeriya sun fatattake su.

Kara karanta wannan

Sabon farmakin Zamfara: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata da diyar lakcara

Bukar Bulama, wani mazaunin garin Buni Yadi, ya shaidawa jaridar TheCable cewa mafarauta ne suka taimaka wa sojojin a yayin wannan mummunan hari.

A cewarsa, sojojin sun kama biyar daga cikin maharan tare da kwato wata motar sulke ta 'yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel