Gwamna El-Rufai ya ba da sandar sarauta ga basaraken gargajiya na garin Lere

Gwamna El-Rufai ya ba da sandar sarauta ga basaraken gargajiya na garin Lere

  • Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya ziyarci masarautar garin Lere domin ba sarkin garin sandar sarauta
  • A jawabansa, gwamnan ya kuma roki sarkin da ya zama mai koyi da marigayi tsohon sarkin da ya gada
  • Hakazalika, ya yiwa garin Lere alkawarin kawo sashin ilimin gona na jami'ar Kaduna yankin nan ba dadewa ba

Lere, Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, a ranar Laraba 29 ga watan Disamba, ya mika wa sabon Sarkin Lere, Suleiman Umaru sandar sarauta.

Malam Umaru, wanda Injiniya ne, ya gaji kawunsa, marigayi Sarki Abubakar II, wanda ya rasu a farkon wannan shekarar.

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru ElRufai ya nada sarkin Lere
El-Rufai ya ba da sandar sarauta ga basaraken gargajiya na yankin Lere | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

A yayin jawabinsa a wurin taron, Mallam El-Rufai ya yi kira ga sabon sarkin da ya yi koyi da magabacinsa marigayi Abubakar, wanda shi kuwa janar din soja ne mai ritaya wajen hidimtawa al'umma.

Kara karanta wannan

Minista ya tona asiri, ya ce Jonathan bai bar wa Buhari komai a asusun Najeriya ba

A cewar gwamnan:

“Ina horonka da ka yi koyi da marigayi Sarki Abubakar II, ka mulki mutanen Lere da tsoron Allah da adalci."

Gwamnan ya kuma yi wa al’ummar Lere alkawarin cewa nan ba da dadewa ba zai kaddamar da ginin sashin ilimin gona na Jami’ar Jihar Kaduna da ke Lere.

Sabon sarkin, ya gode wa gwamnan bisa karramawar da ya yi masa, inji rahoton Premium Times.

Bikin ya biyo bayan wata babban bikin durbar da masarautar ta shirya.

Dawakai masu ado da mahaya cikin jerin gwano sun tarbi sabon sarkin da dukkan manyan baki da suka halarci taron.

Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli, da manyan jami'an gwamnati abokai da masu fatan alheri ne suka halarci bikin.

Mazauna yankin da suka zanta da manema labarai sun ce zabar Malam Umaru a matsayin sabon sarki abin farin ciki ne ga daukacin al’ummar masarautar.

Kara karanta wannan

Korona ta barke a Aso Rock: Garba Shehu, Lai Mohammed, Dogarin Buhari duk sun kamu

Wani mazaunin yankin ya ce:

“Mu a Lere, muna cike da farin ciki a yau. Mun gode wa gwamna da ya zo nan a yau don shaida wannan tarihi. Sarki Umaru na kaunar kowa kuma muna farin cikin ganinmu a yau."

Gwamna Ganduje ya gabatar da sandan girma ga sarkin Bichi, Nasiru Ado-Bayero

A baya mun kawo muku rahoton cewa, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, a ranar Asabar, ya mika sandar girma ga Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado-Bayero, a matsayin Sarkin Bichi na biyu.

Masarautar ta Bichi tana daya daga cikin sabbin masarautun da gwamnatin Ganduje ta kirkiro.

Sauran sabbin masarautun da aka kirkiro sune Rano, Gaya da Karaye, baya ga majalisar masarautar Kano da ake da ita.

A ranar Juma'a ne Sarkin ya aurawa 'yarsa dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf.

Da yake jawabi bayan gabatar da sandar girma ga sarkin, Ganduje ya ce gwamnatin jihar ta yaba da gudummawar da masaratun ke bayarwa don inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Kara karanta wannan

Sanata Shehu Sani ya gwangwanje jami'an kan hanya da kyautukan kirsimeti a Kaduna

Ganduje ya ce gudummawar da sarautar gargajiya suka bayar, ya sanya gwamnati ta kirkiro karin masarautun, da nufin fadada ci gaba zuwa yankunan da ke kasa.

A wani labarin, mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk, ya yi magana kan dalili da yasa aka nada Yusuf, dan Shugaba Muhammadu Buhari sarauta a Daura, rahoton Daily Trust.

Yusuf, wanda shine da namiji tilo na Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Asabar, aka nada shi sarautar Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa.

Da ya ke jawabi a fadarsa yayin bikin nadin sarautar sabbin hakimai hudu, a ranar Alhamis, sarkin ya ce nadin zai hana Talban yawo zuwa Abuja da Yola, garin mahaifiyarsa, bayan wa'adin mulkin Buhari ta kare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel