Sanata Shehu Sani ya gwangwanje jami'an kan hanya da kyautukan kirsimeti a Kaduna

Sanata Shehu Sani ya gwangwanje jami'an kan hanya da kyautukan kirsimeti a Kaduna

  • Dan siyasa kuma dan fafutuka, haifaffen Kaduna, Shehu Sani, ya sanya murmushi a fuskokin masu lura da ababen hawa a jihar Kaduna
  • Tsohon dan majalisar dattawan daga Kaduna a yayin shagalin kirsimeti ya raba wa jami’an da ke bakin aiki kyautukan Kirsimeti
  • 'Yan Najeriya a Facebook sun mayar da martani ga irin wannan karimcin Sani inda suka bayyana shi da cewa ya zama misali na shugaba nagari

Kaduna – A wani yanayin da ya jawo hankalin jama'a, Sanata Shehu Sani ya raba wa masu kula da zirga-zirgar ababen hawa a jihar Kaduna kyautukan Kirsimeti.

Yayin da Kiristocin Najeriya ke bikin Kirsimeti tare da biliyoyin takwarorinsu a fadin duniya, Sani ya yanke shawarar gwangwaje jami’an yayin da suke bakin aiki.

Shehu Sani yayin rabon Kirsimeti
Sanata Shehu Sani ya gwangwanje jami'an kan hanya da kyautukan kirsimeti a Kaduna | Hoto: Shehu Sani
Asali: Facebook

Legit.ng ta gano cewa tsohon dan majalisar ya bayyana aikin nasa ne a ranar Asabar, 25 ga watan Disamba a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook. A cewarsa, jami’an ba su tambaye shi, kawai ya yi niyyar yin hakan ne.

Kara karanta wannan

Muryar jami'in EFCC ya na sanar da yadda Malami ke kange masu cin rashawa ta bayyana

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martani ya biyo bayan kyautukan da Sani ya raba

A halin da ake ciki, wasu 'yan Najeriya sun mayar da martani kan wannan aiki na Sanata Sani.

Onoja Anthony Adama ya ce:

"Kana da tabbacin zama gwamnan Kaduna na gaba. Kai mutum ne mai son jama'a."

Amarachi Sunny Ucheji ya ce:

"Shugaba mafi kyau a jihar Kaduna! Karin Alheri Alhaji!"

Uthman Dangambo ya rubuta:

"Aiki mai kyau aboki."

Zulaiha Sani tace

"Shugaban kirki, ka ci gaba da tsalle."

Yahaya Umar yace:

"Shugaba nagari kenan."

A wani labarin, gomman mabiya akidar Shi'a sun halarci bikin Kirismeti a Cocin HEKAN dake garin Zariya jihar Kaduna ranar Asabar, 25 ga Disamba, 2021.

Shugaban Cocin, Hakila Darmah, wanda ya karbi bakuncinsu ya bayyana farin cikinsa bisa wannan karamci, rahoton NAN.

Yace:

Kara karanta wannan

El-Rufai ya tura sako ga 'yan Kaduna, ya ce su gaggauta cika shirin tallafin Korona

"Gaskiya na yi farin ciki sosai ganin yadda suka yi tunani irin wannan na kawo mana ziyara ranar murnar Kirismeti"

Asali: Legit.ng

Online view pixel