Gwamna Ganduje ya gabatar da sandan girma ga sarkin Bichi, Nasiru Ado-Bayero
- Daga karshe Gwamna Ganduje ya gabatar da sandar girma ga Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado-Bayero
- Da yake jawabi yayin gabatar da sandar, Gwamna Ganduje ya yabawa cibiyoyin sarauta na jihar
- A halin da ake ciki, sarkin ya bukaci mutanen masarautar da su kara himma wajen shigar da yaransu cikin tsarin ilimin boko
Bichi, Kano - Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, a ranar Asabar, ya mika sandar girma ga Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado-Bayero, a matsayin Sarkin Bichi na biyu.
Masarautar ta Bichi tana daya daga cikin sabbin masarautun da gwamnatin Ganduje ta kirkiro.
Sauran sabbin masarautun da aka kirkiro sune Rano, Gaya da Karaye, baya ga majalisar masarautar Kano da ake da ita.
A ranar Juma'a ne Sarkin ya aurawa 'yarsa dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake jawabi bayan gabatar da sandar girma ga sarkin, Ganduje ya ce gwamnatin jihar ta yaba da gudummawar da masaratun ke bayarwa don inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Ganduje ya ce gudummawar da sarautar gargajiya suka bayar, ya sanya gwamnati ta kirkiro karin masarautun, da nufin fadada ci gaba zuwa yankunan da ke kasa.
Ya bukaci Sarkin da sauran sarakunan jihar, da su ci gaba da ba gwamnati gudunmawa wajen samar da tsaro ga dukiyoyi da rayukan jama'a.
Gwamnan ya bukaci Sarkin da ya ci gaba da zama uba ga duk talakawansa ba tare da nuna bambanci ba.
A jawabinsa na mika godiya, sabon Sarkin, yayi alkawarin yin adalci ga dukkan mutanen masarautar.
Hotuna da bidiyoyin liyafar cin abinci dare na auren Yusuf da Zahra, Ali Jita da Breaker sun bajekoli
Ado-Bayero ya bukaci mutanen masarautar da su kara himma wajen shigar da yaransu cikin tsarin ilimi na asali.
Hotunan bikin mika wa sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma
A baya mun kawo cewa urukin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, zai amshi sandar girma a yau Asabar, 21 ga watan Agusta.
Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan daura auren ‘yarsa, Zahra Bayero da dan Shugaban kasa, Yusuf Buhari.
Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa tuni aka fara bikin wanda ke gudana a Masarautar Bichi da ke Jihar Kano.
Asali: Legit.ng