Sarkin Daura: Mun ba Yusuf Buhari sarauta ne don kada ya riƙa gararamba a Abuja bayan Buhari ya sauka mulki

Sarkin Daura: Mun ba Yusuf Buhari sarauta ne don kada ya riƙa gararamba a Abuja bayan Buhari ya sauka mulki

  • Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk ya magantu kan dalilin da yasa aka nada Yusuf Buhari da sarautar Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa
  • Sarkin ya bayyana cewa ba sa son Yusuf Buhari ya yi ta zuwa birnin tarayya Abuja da Yola (garin mahaifiyarsa) bayan Shugaba Buhari ya sauka daga mulki a 2023
  • Alhaji Farouk ya kuma kara da cewa Buhari ya kawo alheri da dama zuwa Daura da suka hada da Jami'a, Kwalleji, Tituna da wasu abubuwa don haka suka bawa Yusuf sarauta matsayin tukwici

Jihar Katsina - Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk, ya yi magana kan dalili da yasa aka nada Yusuf, dan Shugaba Muhammadu Buhari sarauta a Daura, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Jerin duka 'Yan tawagar Shugaba Buhari yayin da ya bar Najeriya zuwa taro a Turkiyya a yau

Yusuf, wanda shine da namiji tilo na Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Asabar, aka nada shi sarautar Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa.

Sarkin Daura: Mun ba Yusuf Buhari sarauta ne don kada ya riƙa gararamba a Abuja bayan Buhari ya sauka mulki
Sarkin Daura ya bayyana dalilin da yasa aka nada Yusuf Buhari sarauta a Katsina. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Dalilin da yasa muka nada Yusuf Sarauta, Sarkin Daura

Da ya ke jawabi a fadarsa yayin bikin nadin sarautar sabbin hakimai hudu, a ranar Alhamis, sarkin ya ce nadin zai hana Talban yawo zuwa Abuja da Yola, garin mahaifiyarsa, bayan wa'adin mulkin Buhari ta kare.

Ya ce:

"Ko da baka kaunar Buhari, kan san cewa Daura a yanzu ta banbanta da yadda ta ke shekaru shida da suka gabata. Don haka, mun masa tukwici kan karamcin da ya yi mana, mun bawa dansa daya tak, Yusuf, sarautar Talban Daura. Hakan zai hana shi yawo zuwa Yola (garin mahaifiyarsa) da Abuja.

Kara karanta wannan

Ba dan Buhari ba da tuni Najeriya ta zama daular muslunci, inji Lai Mohammed

"Daga Jami'ar Fasahar Zirga-Zirga zuwa Kwallejin Fasaha ta Tarayya, ga tituna da wasu manyan ayyukan raya kasa da cigaba. A yau, Daura ta fi wasu jihohin Najeriya a bangaren cigaba."

Sarkin ya cigaba da cewa akwai 'yan asalin Daura masu yawa da suka taka rawan a zo a gani, amma ba kowa ke son sarauta ba, amma dai Buhari ya ciri tuta a cikinsu, Daily Trust ta ruwaito.

Sabbin mutane hudun da aka yi wa nadin sarauta sun hada da Armaya'u Bello, sabon Sarkin Gabas Kwasarawa da Dagajin Kauyen Fatautawa da wasu saura.

Wasu jiga-jigai a arewa sun so su hana APC tsayar da Buhari takara a 2015, Bisi Akande

A wani labarin, Bisi Akande, tsohon shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya ya ce akwai wasu shugabannin arewa da su ka nemi kada jam’iyyar ta tsayar da Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takara a 2015, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan da SSS suka fatattaki masu zanga-zanga a Katsina, Masari ya kai kara wajen Buhari

A littafin tarihin rayuwarsa na “My Participation”, Akande ya ce akwai wasu sanannun shugabannin gargajiya da su ka so a hana tsayar da Buhari a matsayin dan takara don gudun janyo wa arewa matsaloli.

Marubucin ya kara da cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya nemi shugabannin jam’iyyar APC kada su kuskura su tsayar da Buhari a matsayin dan takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel