Korona ta barke a Aso Rock: Garba Shehu, Lai Mohammed, Dogarin Buhari duk sun kamu

Korona ta barke a Aso Rock: Garba Shehu, Lai Mohammed, Dogarin Buhari duk sun kamu

  • Cutar Korona ta sake ballewa a fadar Shugaban kasa Aso VIlla yayinda ake shirin bikin Kirismeti
  • Kawo yanzu, an tabbatar da cewa kimanin mutum hudu suka kamu da sabon nauyin cutar 'Omicron'
  • Daga ciki akwai wanda yayi rigakafin Korona har sau uku amma gwaji ya nuna ya kamu

Abuja - Sabuwar nauyin cutar Korona ta barke a fadar Shugaban kasa, Aso VIlla, inda manyan hadiman Shugaba Buhari da manyan jami'an gwamnati suka kamu da cutar.

Premium Times ta bankado cewa sakamakon gwajin da aka gudanar ya nuna cewa akalla manyan na kusa da Buhari guda hudu sun kamu da cutar.

Daga cikinsu akwai Sakataren din-din-din na fadar Shugaban kasa, Tijjani Umar; Dogarin Buhari, ADC Kanal Yusuf Dodo; CSO Aliyu Musa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu.

Kara karanta wannan

Mutum 7 sun rasa rayukansu a mumunan hadarin da ya auku ranar Kirismeti

Hakazalika akwai Ministan Labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, shima sakamako ya nuna Korona ta hau shi.

Dogarin Buhari duk sun kamu
Korona ta barke a Aso Rock: Garba Shehu, Lai Mohammed, Dogarin Buhari duk sun kamu Hoto: ChannelsTV
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya kara da cewa a ranar Laraba, an yakice Garba Shehu da wasu daga taron majalisar zartaswa ranar Laraba yayinda sakamakon gwajin PCR ya fito.

Garba Shehu ya tabbatar da cewa lallai ya kamu da cutar a sakon da Premium Times tace ta gani.

Yace:

"Ban da tabbacin wadannan mutanen da ka ambata amma na kamu da sabon nauyin cutar maras tsanani. Tun farko ban ji komai ba, la'alla saboda na yi rigakafi sau uku ne, amma yanzu garau nake ji."
"Amma matsalar cutar nan itace sai abinda masana kimiya suka fada cewa kaji sauki. Yanzu dai ina killace kuma zan koma in sake gwaji don ganin ko har yanzu akwai cutar ko ta tafi."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun mamaye dajin Falgore, a kawo dauki: Ganduje ya kai kuka wajen Buhari

Duk yunkurin ji daga bakin Lai Mohammed, Femi Adesina, Tolu Ogunlesi, ya ci tura.

Amma majiyoyi masu karfi sun bayyana cewa dukkan jami'an da suka kamu na killace su kuma ana kula da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel