Minista ya tona asiri, ya ce Jonathan bai bar wa Buhari komai a asusun Najeriya ba

Minista ya tona asiri, ya ce Jonathan bai bar wa Buhari komai a asusun Najeriya ba

  • Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya yi wani sabon fallasa dangane da kudaden da Goodluck Jonathan ya bari a shekarar 2015
  • A cewar Amaechi, kudaden da tsohon shugaban kasar ya bari, ba za su wadatar da al’ummar kasar nan akalla na makwnni uku ba
  • Amaechi ya ce jami’an fadar shugaban kasa ne suka sanar da shi cewa a lokacin babu wani abu da ya rage a cikin baitul malin kasa

Rotimi Amaechi, Ministan Sufuri ya ce kudaden da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bar wa Najeriya a lokacin tafiyarsa a rl2015 ba su isa tafiyar da harkokin kasar na tsawon makwani uku ba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Amaechi wanda tsohon shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ne ya bayyana hakan ne a wani shirin gidan talabijin a ranar Juma’a, 24 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Buhari ga hafsoshin tsaro: Ku murkushe Boko Haram kafin 2023

Minstan Buhari, Ameachi
Minista ya tona asiri, ya ce Jonathan bai bar wa Buhari komai a asusun Najeriya ba | Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya yi ikirarin cewa yayin da yake jagorantar gwamnonin, jami’an fadar shugaban kasa sun sanar da shi cewa kusan babu wani abu da ya rage a cikin baitul malin kasar a baya.

Amaechi ya kara da cewa talauci na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da rashin tsaro, barnar ‘yan bindiga da sauran su a gwamnatin Buhari da Osinbajo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan ya ce:

"Yayin da kuke magana game da 'yan bindiga da duk wadannan mutanen da suke kashewa. Tambaya ce akan talauci. Kuma wannan talauci bai fara a wannan mulkin ba. Kar ku manta ana sayar da gangar mai a kan dala 110, 114, 115, a lokacin da wannan gwamnati ta hau mulki, mai ya fadi zuwa dala 28, kuma tun lokacin bai haura dala 80 kan kowacce ganga ba.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnoni 6 suka hana Majalisa juyawa Shugaban kasa baya a kan kudirin gyara zabe

“A matsayina na tsohon shugaban kungiyar gwamnoni, jami’an tsaro sun shaida min a wani taro da tsohon shugaban kasa ya jagoranta ciki har da tsohuwar ministar kudi cewa a kowane lokaci dole ne gwamnati ta bar kudin ko ta kwana idan har Najeriya ta fada cikin yaki wanda zai dauki watanni shida.
“A lokacin da muka zo, ba su bar kudin da za su iya kai mu tsawon makwanni uku ba. Kuma ina magana a wancan lokacin a matsayina na shugaban kungiyar gwamnonin.”

Muna goyon bayan kara farashin man fetur dari bisa dari, Yan kasuwan Mai IPMAN

Dangane da karin farashin man fetur a bana, kungiyar yan kasuwan mai masu zaman kansu IPMAN sun bayyana cewa tana maraba da shirin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya zata yi a 2022.

Shugaban kungiyar, Mr Chinedu Okoronkwo, ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai NAN ranar Juma'a a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

Mr Okoronkwo, ya bayyana cewa ai tun ranar 16 ga Agusta, 2021 Shugaban kasa ya soke tallafin mai tun da ya rattafa hannu kan sabuwar dokar PIA.

A cewarsa:

"Mu a matsayinmu na yan kasuwa mun dade muna baiwa Gwamnati shawarar cire tallafin mai saboda babu amfani ga cigaba."

Shugaba Buhari ya tura wasika ga majalisa kan kudirin gyara kundin zabe

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da kudirin yin kwaskwarima ga dokar zabe ta 2021, jaridar This Day ya rahoto.

A wata wasika da ya aikewa shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, shugaban ya ce halin da kasar ke ciki ba zai ba shi damar sanya hannu kan kudirin ba.

Daga cikin wasu dalilan kin amincewa da kudirin, shugaban ya bayar da misali da kudaden gudanar da zaben fidda gwanin kai tsaye, kalubalen tsaro na sa ido kan zaben, take hakkin ‘yan kasa da kuma mayar da kananan jam’iyyun siyasa saniyar ware.

Kara karanta wannan

Labari da duminsa: Gobara ta yi kaca-kaca da katafaren kamfani a jihar Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel