Da ɗanyen rogo da masara suka ciyar da mu tsawon sati 2, in ji ɗaliban da masu garkuwa suka sace

Da ɗanyen rogo da masara suka ciyar da mu tsawon sati 2, in ji ɗaliban da masu garkuwa suka sace

  • Wani dalibi mai suna Bolu da ke Jami'ar Tarayya da ke Oyo ya magantu kan mawuyacin halin da suka shiga hannun masu garkuwa
  • Bolu ya ce sun yi karo da masu garkuwar ne a shingen sojoji a jihar Ondo inda suka tisa keyarsu har zuwa jihar Kwara
  • Ya ce tun bayan da suka sace su, babu wani abinci da suka ci illa danyen rogo da masara tsawon mako 2 har sai da aka fanshe su

Oyo - Wani dalibi a Jami'ar Tarayya da ke Jiyar Oyo, mai suna Bolu ya bayyana yadda masu garkuwa suka ciyar da shi da yan uwansa danyen rogo da masara tsawon sati biyu da suke hannunsu, The Nation ta ruwaito.

Bolu ya ce shi da yan uwansa sun shafe makonni biyu tare da masu garkuwar bayan sun kama su a Akure, jihar Ondo, suka kai su jihar Kwara inda suka safe kwanaki a daji kafin aka sako su.

Read also

Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Da ɗanyen rogo da masara suka ciyar da mu tsawon sati 2, in ji ɗaliban da masu garkuwa suka sace
Da ɗanyen rogo da masara suka bamu tsawon sati 2, in ji ɗaliban da masu garkuwa suka sace. Hoto: Daily Trust
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce masu garkuwar sun saka kaya ne irin ta sojoji kuma har motar sintiri suke da shi a bakin titi kamar yadda ya zo a ruwayar The Nation.

Ya bayyana cewa masu garkuwar sun kuma tare wasu motocci guda shida suka sace fasinjojin ciki har da ango da amarya.

A cewarsa:

"Sati biyu da suka wuce, muna dawowa daga Legas. Da muka isa Akure, mun gamu da shingen sojoji. Sun duba motarmu suka ce mu tsaya a ciki. Bayan wasu mintuna, sun ce mu bi su zuwa bariki tare da wasu motoccin shida.
"Wani ango da amarya da ke hanyar zuwa Akure suma an tare su. Sun canja hanya sun kai mu Ekiti daga nan sai Kwara. Mun shafe sati biyu tare da su a daji har sai da aka biya kudin fansa.

Read also

'Yan bindiga sun sace dan uwan hadimin Jonathan da wasu mutum 8 a Kwara

"Mun tsaya a Oyin a Ekiti muka taka zuwa Kabba a Kogi. Daga Kabba suka sa mu a mota zuwa jihar Kwara. Ba mu san inda muke ba. Muna shan ruwan rafi da duk inda muka samu. Danyen rogo da masara kadai muka ci."

Bolu ya cigaba da cewa masu garkuwar sun musu duka sun kuma yi barazanar halaka su a yayin da suke ta canja musu wuri a dajin.

Daga karshe ya ce sun sake su ne bayan wani dan uwansu ya kawo kudin fansa kuma ba su sanar da 'yan sanda ba tunda sun riga sun biya kudin fansa.

Sokoto: Yadda ƴan bindiga suka amshe miliyoyi daga basarake kuma suka ƙi sako waɗanda suka yi garkuwa da su

A wani rahoto daga Sokoto, 'Yan bindiga sun amshe Naira miliyan 2.2 (N2,200,000) a matsayin kudin fansa amma sun ki sakin mutane 20 da su ka sata.

Read also

Tubabbun yan Boko Haram sun yi zanga-zanga, sun gudu daga wuraren da aka ajiyesu

Buzu, na biyu a hatsabibanci daga Bello Turji, duk da an biya shi makudan kudade don sakin mutane 20 da su ka sata a Gatawa ya murje ido ya lamushe kudin babu wani bayani.

Premium Times ta ruwaito yadda ‘yan bindigan su ka aika wa dagacin Burkusuma da sarkin Rafi wasika inda su ka bayyana cewa su na bukatar N20,000,000 a matsayin kudin fansar wadanda su ka sata.

Source: Legit

Online view pixel