'Yan bindiga sun sace dan uwan hadimin Jonathan da wasu mutum 8 a Kwara

'Yan bindiga sun sace dan uwan hadimin Jonathan da wasu mutum 8 a Kwara

  • Miyagun 'yan bindiga sun tsinkayi garin Olla da ke karamar hukumar Isin ta Kwara inda suka sace dan uwan hadimin Jonathan
  • Olujala Adegboja manajan gidan gona ne kuma miyagun sun tare shi yayin da ya ke hanyarsa ta komawa gida da motarsa kirar Hilux
  • Har ila yau, miyagun sun dira wani kamfanin ruwa inda suka tasa keyar mutum takwas duk da mai gidan ruwan, Hajiya Fatima

Kwara - 'Yan bindiga da suka kai shida a daren Asabar sun tsinkayi garin Olla da ke karamar hukumar Isin ta jihar Kwara inda suka sace wani Olujala Adegboja, manajan gona wanda ke kan hanyarsa ta komawa gida.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wanda aka sacen ya na tuka farar mota kirar Toyota Hilux yayin da masu garkuwa da mutanen suka yi masa kwanton bauna sannan suka tasa keyarsa zuwa cikin daji.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna

'Yan bindiga sun sace dan uwan hadimin Jonathan da wasu mutum 8 a Kwara
'Yan bindiga sun sace dan uwan hadimin Jonathan da wasu mutum 8 a Kwara. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Mazauna yankin sun sanar da Daily Trust cewa, wanda aka sace din an fi sanin shi da Oni-Jay kuma ya na da shekaru 56 a duniya. Dan uwan basarake ne kuma jigon PDP, Hon Oluyola Onijala, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Wata majiya wacce ta san kan lamarin ta ce da farko wanda aka sacen ya ki bin masu garkuwa da mutanen amma daga baya sai suka fi karfinsa inda suka fara sarar shi kuma suna harbi a iska domin firgita shi.

"Masu garkuwa da mutanen sun kai farmakin hankalinsu kwance na tsawon mintoci masu yawa.
"An ga motar kirar Toyota Hilux da jini saboda da farko ya ki bin su," majiyar ta kara da cewa.

An gano cewa yankin a halin yanzu suna cikin tashin hankali ballantana kan halin da wanda aka sacen ya ke ciki.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Har cikin fada, 'yan bindiga sun harbe yarima, sun sace gimbiya a arewacin Najeriya

Sai dai, masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan Onijala inda suka bukaci a biya su N200 miliyan kudun fansa kafin su sako shi.

Hakazalika, mutum 7 dauke da makamai sun kai farmaki wani gidan ruwa da ke Sosoki, yankin Alapa da ke karamar hukumar Asa ta jihar Kwara a ranar Asabar.

Sun kwashe mutum takwas daga cikin ma'aikatan wadanda suka hada da mai kamfanin ruwan, Hajiya Fatima Nurudeen.

'Yan bindiga sun sheke maharbi, sun tasa keyar mutum 30 a Niger

A wani labari na daban, yayin da ‘yan bindiga su ka kai farmaki garin Zazzaga da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja, sun halaka mafarauci sannan suka yi garkuwa da fiye da mutane 30. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Bala Kuryas, ya tabbatar da aukuwar lamarin, Daily Trust ta wallafa.

A cewarsa, lamarin ya auku da misalin 2am na Laraba inda ya kara da cewa ‘yan sanda sun bi sawun ‘yan bindigan don ceto wadanda su ka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Borno: Arangama ta da 'yan ta'addan ISWAP a kan titi, Malamin makaranta

Sai dai, Sakataren karamar hukumar Munya, James Jagaba, ya sanar da wakilin Daily Trust ta wayar salula ya ce an yi garkuwa da mutane 68, har da mata da yara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel