Tubabbun yan Boko Haram sun yi zanga-zanga, sun gudu daga wuraren da aka ajiyesu

Tubabbun yan Boko Haram sun yi zanga-zanga, sun gudu daga wuraren da aka ajiyesu

  • Yan ta'addan Boko Haram da suka mika wuya sun ce gaskiya sun gaji da zama waje guda babu aiki
  • Tubabbun sun gudanar da zanga-zanga inda suka lalata dukiyar gwamnati kuma har wasu suka gudu
  • Har yanzu gwamnatin jihar Borno bata yi tsokaci kan wannan abu ba

Borno - Tubabbun yan Boko Haram da suka mika wuya ga Gwamnati sun yi zanga-zanga kan cigaba da ajiyesu waje guda a wasu sansani dake birnin Maiduguri, jihar Borno.

An tattaro cewa wasu daga cikinsu sun gudu daga wuraren da aka ajiyesu.

Majiyoyi sun bayyanawa AFP ranar Alhamis cewa wannan shine karo na hudu da tsaffin ta'addan suke zanga-zanga kan cigaba da tsaresu waje guda ba sa komai.

Daya daga cikin majiyoyin yace,

"Tsaffin yan Boko Haram din sun ce an ajiyesu waje guda tsawon watanni hudu ba su yin komai. Sun ce an raba su da matansu; wasu na da mata uku, wasu hudu."

Kara karanta wannan

Matasan ‘yan Najeriya 4 da suka ginawa iyayensu mata gida, daya daga cikinsu bata kai shekara 15 ba

"Sun lalata sansanin da aka ajiyesu lokacin zanga-zangan. Sunce Gwamnati ta sakesu idan ba tada wani shiri na musamman garesu."

Tubabbun yan Boko Haram
Tubabbun yan Boko Haram sun yi zanga-zanga, sun gudu daga wuraren da aka ajiyesu Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: UGC

Wata majiyar tace kimanin yan Boko Haram 250, mata da yara sun yi zanga-zanga a Gidan Taki inda suka fasa tagogin da kofofin sansanin.

Wani mai taimakawa Sojoji, Konto Garga, yace:

"Yan Boko Haram sun haukace mana da safen nan, sun fasa kofofi, tagogi kuma suna kokarin guduwa."

Wasu sun fara guduwa cikin gari

Jaridar Punch ta tattaro cewa tsaffin yan ta'addan sun gudu daga cikin sansanin.

Majiyar Punch tace:

"Wasu daga cikinsu na guduwa daga sansanin. Sun ce sun gaji da zama waje guda."

Amma kwamishanar harkokin mata, Hajiya Zuwaira Gambo, tace babu zanga-zangar da ta faru a sansanin.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun gudu da kafafunsu yayinda yan acaba suka kai musu hari kan kashe abokinsu

Yan ta'addan Boko Haram 17,000 suka mika wuya kawo yanzu, Kwamdanda Operation Hadin Kai

Tiyata Kwamanda na rundunar “Operation Hadin Kai”, Christopher Musa, ya bayyana cewa adadin yan Boko Haram da suka mika wuya kawo yanzu ya kai 17,000.

Musa ya bayyana hakan ne ranar Juma'a lokacin da ya kai ziyara wajen shugabannin hukumar cigaban Arewa maso gabas, NEDC.

Ya bayyana cewa wannan adadi ya hada da mayaka, iyalansu da kuma wadanda aka tilasta shigar harkar Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel