Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna

  • Masu garkuwa sun halaka Sagir Hamidu tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna
  • Hamidu na cikin matafiya da masu garkuwar suka bude wa wuta ne sannan suka yi awon gaba da wasu matafiyan da dama
  • Majiya da hukumomin tsaro ta tabbatar da mutuwar dan siyasan tana mai cewa yana da cikin wadanda 'yan bindigan suka harbe

Jihar Kaduna - Yan bindiga sun kashe Sagir Hamidu, tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a shekarar 2019, a babban hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Marigayin dan siyasan ya nemi kujerar gwamnan ne a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, APC mai mulkin kasa.

Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna
'Yan bindiga sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Maharan sun bindige shi har lahira ne yayin da suka bude wuta kan matafiya a kusa da Rijana misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi.

Majiya daga jami'an tsaro da suka nemi a boye sunansu sun tabbatar wa Daily Nigerian mutuwarsa suna mai cewa, 'yana daga cikin wadanda suka mutu sakamakon harbin da yan bindigan suka yi.'

Majiyoyi sun ce an bindige fasinjoji da dama da suke nemi su tsere, yayin da wadanda suka bada hadin kai su kuma an tisa keyarwasu zuwa cikin daji.

Wani da ya tsira daga harin kuma ya nemi a boye sunansa ya shaidawa wakilin Daily Nigerian cewa harin ya faru ne a kusa da Rijana.

Ya ce:

"Masu garkuwar sun yi amfani da rashin kyawun hanyar, wanda hakan ya tilastawa motocci tafiya a hankali kuma a hannu guda a titin."

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige bai amsa kirar da aka masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Zamfara: Ƴan bindiga sun yi wa dagaci yankan rago a gaban jama'a, kun kashe wasu 8

A baya kun ji cewa Ƴan bindiga sun yi wa dagacin ƙauye yankan rago sun kuma kashe wasu mutane takwas a Tungar Ruwa a ƙaramar hukumar Anka na jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne a tsakar daren ranar Laraba kamar yadda Premium Times ta ruwaito. Ƴan bindigan sun shafe awanni yayin harin.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Mohammed Shehu ya tabbatar da harin amma bai bada cikakken bayani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel