Sokoto: Yadda ƴan bindiga suka amshe miliyoyi daga basarake kuma suka ƙi sako waɗanda suka yi garkuwa da su

Sokoto: Yadda ƴan bindiga suka amshe miliyoyi daga basarake kuma suka ƙi sako waɗanda suka yi garkuwa da su

  • Yan bindiga su ka lamushe naira miliyan 2.2 na kudin fansar mutane 20 ba tare da sakin su ba
  • Sun tura wasika zuwa ga Hakimin Burkusuuma, Sarkin Rafi su na bukatar a tattara N20,000,000
  • Saidai bayan tattara N2.2m da kuma tura mu su, su Buzu sun yi tsit, har yau ba su saki ko mutum daya ba

Jihar Sokoto - 'Yan bindiga sun amshe Naira miliyan 2.2 (N2,200,000) a matsayin kudin fansa amma sun ki sakin mutane 20 da su ka sata.

Buzu, na biyu a hatsabibanci daga Bello Turji, duk da an biya shi makudan kudade don sakin mutane 20 da su ka sata a Gatawa ya murje ido ya lamushe kudin babu wani bayani.

Sokoto: Yadda 'yan bindiga suka amshe miliyoyi daga basarake kuma suka ki sako wadanda suka yi garkuwa da su
Taswirar Jihar Sokoto. Hoto: Premium Times
Source: Facebook

Read also

Yadda waɗanda aka yi garkuwa da su suka shafe kwanaki 53 sun cin ciyawa

Premium Times ta ruwaito yadda su ka halaka mutane 19 sannan su ka yi garkuwa da mutane 21 a daren da su ka kai farmaki garin Gatawa.

Dama wasika su ka tura wa dagacin kauyen

Premium Times ta ruwaito yadda ‘yan bindigan su ka aika wa dagacin Burkusuma da sarkin Rafi wasika inda su ka bayyana cewa su na bukatar N20,000,000 a matsayin kudin fansar wadanda su ka sata.

Kamar yadda bayanai su ka kammala, majiyoyi 2 ciki har da kanwar daya daga cikin wadanda su ka sata, sun bayyana yadda ‘yan bindiga suka bukaci kudi daga ‘yan uwa da abokan arzikin wadanda su ka sata, sannan su tattara a hannun dagacin kauyen.

Daya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa:

"Buzu ya yanke hukunci a maimakon Turji, ya bukaci a biya ta hannun dagacin kauyen. Sai dai mun bukaci dagacin ya nemi sauki daga wurin su, duk da ya na tsoron kin bin umarnin su, mun bukaci ya nemi ragi daga naira miliyan 20 zuwa naira miliyan 2.”

Read also

Zamfara: Ƴan bindiga sun kashe mutum 19, ciki har da ƙananun yara, sun ƙone shaguna da gidaje

A cewar majiyar, daga baya ‘yan bindigan sun amince da naira miliyan 2.2 amma har yanzu Buzu bai sake ko mutum daya daga cikin wadanda su ka sata ba.

Wata majiya daga Sabon Birni wacce ta bukaci a sakaya sunan ta, ta bayyana cewa an ba ‘yan bindiga kudin amma har yanzu ba su saki ko mutum daya ba.

Kamar yadda ta shaida:

“Yanzu haka wadanda aka sata su na Suruddubu, wanda karkashin ikon Buzu suke. Na samu labarin yadda aka tura wa Buzu naira miliyan 2.2 amma ya nace sai an tura naira miliyan 20 da kuma jarkokin man fetur. Lamarin ya zama abin tsoro.”

Premium Times ta kira kakakin rundunar ‘yan sanda, Sunusi Abubakar amma be dauki wayar ba kuma be bayar da amsar sakon da aka tura ma sa ba.

Yadda 'yan bindiga suka afka wa wani gari a Sokoto yayin da suke neman sojoji

A wani rahoton, 'yan bindiga sun afka Gangara, wani kauye dake karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto a ranar Talata, sun je kai wa sojoji farmaki.

Read also

'Yan bindiga sun kashe mutum 10, sun raunata wasu da dama a sabon harin da suka kai Katsina

‘Yan bindiga sun afka yankin ne bayan bai wuci sa’o’i 48 da suka harbe sojoji 17 a sansanin su da ke Dama ba, duk a karamar hukumar Sabon Birni kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Dan majalisar jihar na yankin, Sa’idu Ibrahim ya ce yanzu ‘yan bindiga su na harin jami’an tsaro ne a yankin.

Source: Legit

Online view pixel