Ango a hannun hukuma: ‘Yan sanda sun yi ram da dan fashi ta hanyar bin diddigin fostar aurensa

Ango a hannun hukuma: ‘Yan sanda sun yi ram da dan fashi ta hanyar bin diddigin fostar aurensa

  • Wani mai shirin zama ango ya shiga hannun 'yan sanda ana saura 'yan kwanaki aurensa
  • An bankado angon wanda ake zargi da hannu a wani fashi da makami da ya wakana da taimakon fostar aurensa da aka manna a wurare
  • A ranar Asabar 13 ga watan Nuwamba, ne ya kamata a daura auren nasa a yankin Sapele da ke jihar Delta

Jihar Delta - A ranar Laraba ne jami'an 'yan sanda suka kama wani direban keken adaidaita, wanda ake shirin daura ma aure a ranar Asabar, 13 da watan Nuwamba.

Pulse Nigeria ta rahoto cewa an damke mai shirin zama angon ne bayan wasu mutane da aka kama bisa laifin fashi da makami sun ambace shi a matsayin shugaban kungiyarsu.

Read also

An tafi har gida an bindige Shugaban kamfanin Three Brothers Mill da matarsa a Jigawa

Ango a hannun hukuma: ‘Yan sanda sun yi ram da dan fashi ta hanyar bin diddigin fostar aurensa
Ango a hannun hukuma: ‘Yan sanda sun yi ram da dan fashi ta hanyar bin diddigin fostar aurensa Hoto: Premium Times
Source: UGC

Rundunar 'yan sandan jihar Delta ta kama wanda ake zargin mai suna Festus bisa zarginsa da hannu a wani fashi da makami a yankin Sapele.

Hotunan auren wanda ake zargin da amaryarsa na ta yawo inda aka manna fostar auren a wurare daban-daban, sannan an bayyana cewa za su shiga daga ciki a ranar Asabar, 13 ga watan Nuwamba a cocin Oghenetega Baptist Church, a Sapele.

Sai dai kuma, bayan yan fashin da aka kama sun tona asiri, sai jami'an 'yan sandan suka bankado direban adaidaitan sannan suka kama shi a unguwarsa.

A cewar wani rahoto daga shafin Correctng.com, shaidu sun ce Festus ya ce bai san komai ba a kan lamarin lokacin da 'yan sandan suka kama shi, inda yace tuggu aka shirya masa.

Read also

Amotekun ta kama mai garkuwa da mutane Labram Ibrahim yayin da yake haukan karya a Ondo

Ya kafra da cewa mutanen da basa son ci gabansa ne ke kokarin shafa masa bakin fenti a laifin da bai san komai ba.

A halin da ake ciki, kamun Festus ya sa zancen aurensa ya sha ruwa sannan ya kunyata amaryarsa wacce da a yanzu sun tare.

Sabuwa fil a leda nake, ban taba sanin ‘da namiji ba har nayi aure – Amarya mai shekaru 55

A wani labari na daban, masu iya magana kan ce da aure da mutuwa duk lokaci ne, hakan ne ya kasance ga wata 'yar Najeriya da ta kusa cire tsammani, domin sai da ta kai shekaru 55 kafin Allah ya bata mijin aure.

Allah ya kulla aure tsakanin matar mai suna Esther Bamiloye da angonta Isaac Bakare mai shekaru 62 wanda shima wannan ne aurensa na farko.

A wata hira da tayi da jaridar Punch, Esther ta bayyana cewar duk da dadewar da tayi ba tare da aure ba, ta yi kokarin ganin ta kare mutuncinta, domin a cewarta bata taba sanin 'da namiji ba kafin aurenta. Ta ce ita budurwa ce sabuwa fil a leda.

Read also

Da Dumi: Malamin addinin musulunci da CSP na bogi na cikin mutum 14 da aka kama kan kutse gidan Mai Shari'a Odili

Source: Legit.ng

Online view pixel