An tafi har gida an bindige Shugaban kamfanin Three Brothers Mill da matarsa a Jigawa

An tafi har gida an bindige Shugaban kamfanin Three Brothers Mill da matarsa a Jigawa

  • Wasu da ake zargin masu kisa ne sun kutsa gidan Alhaji Musa, Shugaban Three Brothers Mills sun halaka shi da matarsa, Hajiya Adama
  • Mai magana da yawun yan sandan jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu ya tabbatar da afkuwar lamarin ga manema labarai a ranar Litinin
  • Shiisu ya ce bata garin ba su dauki komai ba a gidan mamacin amma a yanzu an kama mutum 5 da ake zargi da hannu a kisar gillar

Jihar Jigawa - 'Yan sanda a jihar Jigawa sun tabbatar da kashe wani mutum da matarsa a karamar hukumar Malam madori na jihar da ake zargin masu kisa don a biya su ne suka aikata.

ASP Lawan Shiisu, mai magana da yawun yan sandan jihar Jigawa, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai NAN hakan a ranar Litinin a Dutse.

Kara karanta wannan

Da dumi-daumi: 'Yan bindiga sun kai hari gefen FUT Minna, sun tafka mummunan barna

An tafi har gida an bindige Shugaban kamfanin Three Brothers Mill da matarsa a Jigawa
An tafi har gida an bindige Shugaban kamfanin Three Brothers Mill da matarsa a Jigawa. Hoto: Usman A Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Guardian ta rahoto Shiisu ya ce lamarin ya faru ne a ranar 13 ga watan Nuwamba misalin karfe 2.30 na dare inda wasu da ake zargin bata gari ne suka kutsa gidan mamamcin a kauyen Kebberi suka bindige su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa wadanda ake zargin kwararrun masu kisa ne sun bindige marigayin, mai suna Alhaji Musa da matarsa Hajiya Adama nan take.

Kakakin yan sandan ya ce wadanda ake zargin ba su sata komai ba daga gidan wadanda abin ya faru da su, wanda shine shugaban kamfanin Three Brothers Mill da ke Malammadori.

Ya ce:

"A ranar 13 ga watan Nuwamba misalin karfe 0230hrs, wasu bata gari da ba a san ko su wanene ba sun kutsa gidan wani Alhaji Musa, Manajan kamfanin Three Brothers Rice Mill, suka bindige shi da matarsa Hajiya Adama dukkansu yan kauyen Kebberi a karamar hukumar Malammmadori."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi

A cewarsa an gano kwalin wayoyin salula biyu daga wurin da abin ya faru, ya kara da cewa an kama mutane biyar da ake zargi da hannu kuma ana musu tambayoyi, The Nation ta ruwaito.

Shiisu ya kara da cewa ana cigaba da kokari domin kamo wadanda ake zargi domin su girbi abinda suka shuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel