Malamin addinin musulunci da CSP na bogi na cikin mutum 14 da aka kama kan kutse gidan Mai Shari'a Odili

Malamin addinin musulunci da CSP na bogi na cikin mutum 14 da aka kama kan kutse gidan Mai Shari'a Odili

  • Rundunar yan sandan Nigeria ta yi holen wasu jami'an tsaro na bogi 14 da ake zargi da kutse a gidan Mai shari'a Odili a Abuja
  • Kakakin yan sandan Nigeria, Frank Mba, a ranar Alhamis ya ce cikin wadanda aka kama akwai dan jarida da malamin addinin musulunci
  • Mba ya kuma ce akwai sauran wasu mutum 10 da ake zargi da hannu a lamarin cikinsu akwai sojoji biyu, ana cigaba da nemansu

Abuja - Jami'an yan sandan Nigeria sun kama 'yan sandan bogi su 14 da suka kai hari gidan Mai Shari'a Mary Odili a ranar 29 ga watan Oktoba, Daily Trust ta ruwaito.

Jami'an dan sanda mai kumamin sufritanda, CSP Lawrence Ajojo da aka ce shi ya jagorancin yan sandan ya bayyana cewa shi ba dan sanda bane.

Kara karanta wannan

Asirin kuɗi: An kama wani mutum da ya haɗa baki da malamin addini mai shekaru 95 don kashe ɗan cikinsa

Da Dumi-Dumi: An cafke jami'an 'bogi' su 14 da suka yi kutse gidan Odili
An cafke jami'an 'bogi' su 14 da suka yi kutse gidan Odili. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ake holen wadanda ake zargin a ranar Alhamis a sashin binciken manyan laifuka, CID, Garki Abuja, Kakakin yan sanda Frank Mba ya ce wadanda suka aikata laifin suna da sana'o'i daban-daban.

A hirar da ya yi da manema labarai yayin holen, DSP na bogi wato Ajojo ya bayyana cewa shi fa ba jami'in rundunar yan sandan Nigeria bane.

Mba ya ce cikin wadanda aka kama akwai dan jarida, da wani malamin addinin musulunci, sannan akwai wasu goma cikin wadanda ake zargin amma ba su shigo hannu ba.

Ya ce:

"Sufeta Janar na rundunar yan sandan Nigeria ya bada umurnin yin sahihin bincike a kan lamarin."

Tun da farko, Ministan shari'a kuma Antoni Janar ya rubuta wasika zuwa ga ofishin IGP yana neman a yi bincike kan lamarin domin gano wadanda ke da hannu da manufarsu.

Kara karanta wannan

Da dumi-daumi: 'Yan bindiga sun kai hari gefen FUT Minna, sun tafka mummunan barna

Daga bisani aka tura binciken zuwa sashin binciken bayannan sirrri na yan sandan bisa umurnin IGP.

Yadda abin ya faru

A ranar 30 ga watan Oktoba ne wasu jami'an tsaro da suka hada da sojoji da yan sanda suka kutsa gidan alkalin kotun kolin kan zargin ana aikata abubuwan da suka saba wa doka a gidan.

Wani Lawrence Ajodo - da ya ce shi sufritandan yan sanda ne ya gabatar da takardan izinin binciken - amma yanzu an gano jami'in bogi ne.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa takardan izinin bincien da yan sandan suka gabatar a gidan Odili yana dauke da adireshin wani gida ne daban.

Abubakar Malami, Antoni Janar da Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC sun ce ba sune suka bada umurnin yin binciken ba.

Wata kotun Majistare da ke Abuja ita ma ta soke takardan izinin binciken da jami'an tsaron suka nuna a gidan kafin su shiga.

Daga nan ne sufeta janar na yan sandan Nigeria, Usman Baba ya bada umurnin a yi bincike.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel