Sabuwa fil a leda nake, ban taba sanin ‘da namiji ba har nayi aure – Amarya mai shekaru 55

Sabuwa fil a leda nake, ban taba sanin ‘da namiji ba har nayi aure – Amarya mai shekaru 55

  • Wata amarya mai shekaru 55 da bata taba yin aure ba ta magantu a kan yadda Allah ya tuna da ita bayan lokaci mai tsawo
  • Amaryar mai suna Esther Bamiloye ta shiga daga ciki tare da angonta mai suna Isaac Bakare mai shekaru 62 wanda shima bai taba yin aure ba
  • Esther ta bayyana cewa dadewar da tayi ba tare da aure ba bai sa ta zubar da mutuncinta ba domin a cewarta ta kai budurcinta gidan aurenta

Masu iya magana kan ce da aure da mutuwa duk lokaci ne, hakan ne ya kasance ga wata 'yar Najeriya da ta kusa cire tsammani, domin sai da ta kai shekaru 55 kafin Allah ya bata mijin aure.

Allah ya kulla aure tsakanin matar mai suna Esther Bamiloye da angonta Isaac Bakare mai shekaru 62 wanda shima wannan ne aurensa na farko.

Kara karanta wannan

Ban taba sanin cewa zan shahara haka ba - Azeema gidan Badamasi

Sabuwa fil a leda nake, ban taba sanin ‘da namiji ba har nayi aure – Amarya mai shekaru 55
Sabuwa fil a leda nake, ban taba sanin ‘da namiji ba har nayi aure – Amarya mai shekaru 55 Hoto: Punch
Asali: UGC

A wata hira da tayi da jaridar Punch, Esther ta bayyana cewar duk da dadewar da tayi ba tare da aure ba, ta yi kokarin ganin ta kare mutuncinta, domin a cewarta bata taba sanin 'da namiji ba kafin aurenta. Ta ce ita budurwa ce sabuwa fil a leda.

Ta kuma bayyana cewa bata taba yin soyayya ba har zuwa aurenta, domin a cewarta a lokacin da ta shirya ma aure sai ya zamana babu wani namiji da ya tunkareta da sunan hakan.

Ta ce:

"Shaidan ya so hana ni yin aure. A lokacin da nake ganin na shirya, babu wani namiji da ya zo. Ina ta jiran Allah ya yi ikonsa har sai da na kai shekaru 55. Ban taba soyayya da wani ba har nayi aure. Da farko, na zata matsalar daga tsohon cocina ne sai na bar cocin, amma ina mika godiya ga Allah. Ya cika mun burina a sabon cocina kuma duk wani shamaki ya kau."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa har yanzu bata dage dakatarwar Twitter ba

Game da ko ta taba yin soyayya da bai kai ga aure ba, matar ta ce:

"A'a, ban taba soyayya ba a baya kafin nayi aure. Na yi rayuwa mai tsafta a zamanin da nake makaranta. Ban taba kowani soyayya ba. Na karbi Yesu da wuri a rayuwa kuma a lokacin da nake a matsayin daliba, ban ma taba tunanin hakan ba, domin na san ban shirya ba a lokacin."

Ta bayyana cewa ta hadu da angon nata ne a wani taro da aka yi a Ilesa, inda tace Allah ne ya tsara komai da komai.

Esther ta kuma bayyana cewa da haduwarsu da kulla auren duk ya zo ne a dan kankanin lokaci. Sannan ta nuna godiya ga Allah da ya tuna da ita bayan lokaci mai tsawo.

Da ina da iko, da na wajabtawa maza auren mata biyu – Jami’ar bincike

A wani labarin, wata jami'ar bincike ta bayyana cewa da ace tana da iko, toh da za ta wajabtawa maza auren mata biyu domin rage yawan zinace-zinace da lalata.

Kara karanta wannan

Jaruma Rahama MK, matar gwamna a fim din Kwana Casa'in ta yi auren sirri

A cewar matar 'yar kasar Kenyan, Jame Mugo, dabi'ar magidanta na yin lalata da yan mata a wajen gidajen aurensu na karuwa a kullun.

Matar ta koka da yadda maza mazinata ke barin yan matansu ba tare da komai ba sannan su koma ga wasu bayan sun gama cin moriyar ganga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel