Amotekun ta kama mai garkuwa da mutane Labram Ibrahim yayin da yake haukan karya a Ondo

Amotekun ta kama mai garkuwa da mutane Labram Ibrahim yayin da yake haukan karya a Ondo

  • Jami’an Amotekun sun yi ram da wani da ake zaton mai garkuwa da mutane ne, Labram Ibrahim, a jihar Ondo
  • Kafin kamun nasa, Ibrahim ya tubure yana haukan karya, inda yanayin shigarsa ya ja hankalin mutanen da ke wajen
  • An kama shi ne a lokacin da wata bakar motar Jeep ta tsaya domin daukarsa

Jihar Ondo - Jami’an tsaron Amotekun reshen jihar Ondo, sun kama wani da ake zaton mai garkuwa da mutane ne mai suna Labram Ibrahim.

Ibrahim mai shekaru 30 yana karyan hauka ne lokacin da aka kama shi, PM News ta rahoto.

Amotekun ta kama mai garkuwa da mutane Labram Ibrahim yayin da yake haukan karya a Ondo
Amotekun ta kama mai garkuwa da mutane Labram Ibrahim yayin da yake haukan karya a Ondo Hoto: Amotekun
Asali: Facebook

An kama shi a garejin Akure da ke garin Ondo, hedkwatar karamar hukumar Ondo ta yanma da ke jihar, bayan zargin yanayin shigarsa da tafiyarsa.

Kara karanta wannan

Borno: Dan majalisa a ya bayyana yadda 'yan ISWAP suka kone gidan da ya ginawa dan uwansa

A bisa ga rahotanni, Jami’an Amotekun da ke yankin, wadanda ke ta lura da shi, sun far masa lokacin da wasu mutane ke shirin daukarsa a cikin wata bakar motar jeep.

Wani idon shaida wanda yayi ikirarin cewa shi mai talla ne a garejin, ya ce:

“Kafin kamun nasa, an lura yana ta tafiya tamkar mai tabin hankali zuwa da kuma daga garejin Akure zuwa mararrabar Itanla kafin wata bakar motar Jeep ta yi fakin a kusa da shi da nufin daukarsa.
“Yanayinsa ya haifar da zargi wanda ya sa mutanen da ke yankin suka hadu sannan suka yi masa duka.”

A halin da ake ciki, wanda ake zargin ya fallasa cewa shi ba mahaukaci bane, amma yana yi wa wani Rabiu Adamu aiki a Akure, babbar birnin jihar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari Kaduna, sun kashe mutane

Ibrahim wanda ya yi ikirarin cewa shi dan Sokoto ne, ya bayyana cewa Rabiu, surukinsa, ya dauke shi zuwa garejin motar Akure sannan ya sanya shi a motar da za ta garin Ondo.

Ya ce:

“Mutumin ya biya direban N700 sannan daga bisani ya bani N1500 don na shiga motar da za ta je Ore sannan daga Ore zuwa Epe inda zan yi aiki. Bai fada mani irin aikin da yake so nayi ba.
“Rabiu ya zo ta baya a bakar motar Jeep dinsa tare da wasu mutane uku a ciki. Ya fada mani na cire sim dina sannan na sa shi a shataletalen garejin Akure sannan na tafi Ore kafin aka kama ni a Itanla saboda yanayin shiga na.”

Jami’an Amotekun a garin Ondo sun bayyana cewa sun shiga aiki domin kama mamallakin bakar jeep din da sauran mutane uku a Akure domin ci gaba da bincike.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

Amotekun sun kama ‘yan bindiga 18 dauke da bindigogi da makamai 500 a motoci uku

A wani labarin, Jami'an tsaron Amotekun reshen jihar Ondo, sun kama motocin bas uku cike da 'yan bindiga 18 da kuma makamai, jaridar Punch ta rahoto.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren labaran gwamnan jihar Ondo, Olabode Richard Olatunde ya saki a ranar Juma'a, 5 ga watan Nuwamba.

Taken sanarwar ita ce: 'Da dumi-dumi: Amotekun reshen Ondo ta kama yan bindiga dauke da bindigogi da makamai 500 a cikin motocin bas uku.'

Asali: Legit.ng

Online view pixel