Wani babban dan wasan barkwanci na Najeriya ya rasa budurwar shi.

Wani babban dan wasan barkwanci na Najeriya ya rasa budurwar shi.

–Yadda aka yi dan wasan barkwanci ya rasa budurwarshi akan N200,000.

-Mai makon a taya babban dan wasar barkwanci na Najeriya murnar zagayowar haihuwar shi, daya daga cikin abokanshi yayi amfani da shafinsa na instagram inda yake bayyana yadda dan wasan barkwanci ya rasa budurwarshi ga wani mai kudi.

Wani mutum da aka bayyana a matsayin uncle speed of Africa a instagram ,ya sa hoton AY da tohuwwar budurwarshi sai yayi rubutu kamar haka’’ nasan AY ! AY hazikin mai wasar barkwanci . AY ya samu cigaba sosai a rayuwar shi, amma da kuna jin haushin dadadan labarunsa, amma bari in fada maku asalin labarinsa.

Labarin ya fara daga makaranta , duk da yana ta fadi ta shi dan ya samu ya tsira, amma abubuwa basu tafi mai yadda ya dace ba. Abin yayi rashin dadi lokacin da budurwarshi da ya so ya aura ta kawo mai ziyara wani yammaci.

Wani babban dan wasan barkwanci na Najeriya ya rasa budurwar shi.

‘’AY, ta fad cikin rada a kunenshi ,a hankali , kasan ina sonka , amma yadda harkokin rayuwarka suke tafiya a sannu ne, bazan iya cigba da zama da kai a haka ba. Sai ta rungume AY , ta mai sunbata ta karshe, ta sake shi, sai ta cigaba da tafiyar yanga tana tunkarar wata mota …………kawai ta tafi abinta. Ashe wani babban mutum ne ya kawo ta dan ta rabu da AY, Amma abin ban haushi wannan mutumin da ya kawota shi yaba AY N200,000 dan ya bar budurwarshi, AY yaki indab yace shi soyayyarshi bata sayarwa bace, gashi yanzu ta tafi.

AY yayi kuka sosai. Inda ya cigaba da bayyana hazakarshi , maganar gaskiya ze iya kasancewa abubuwan shi a sannu suke, amma ba wanda ze iya ma rayuwa garaje, amma duk da haka bai gajiya ba. A hankali ya koma Lagos, amma bai gajiya ba har ya zama mai taimaka ma Ali Baba , haka ya cigaba har sai da ya zama dan wasar barkwanci , a hankali , a sannu AY ya cigaba da zama babba a Africa.

Haka ya cigaba tun yana haya a Iponri,Agudo da Ikorudo har ya mallaki gida a Lekki. A sannu har yayi wasar barkwanci da aka fi kallo a youtube amma be gajiya ba sai da yayi 30dayus in Atlanta wanda ya zamo wasar da aka fi kallo a nahiyarv Africa .

Kar ka damu da rashin saurin samunka, in dai har baka gajiya ba, to wata rana zaka kaiga gaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng