Yadda Sahar Facebook Ta Kulla Auren So da Kauna a Jihar Kano
- Wata matashiyar yar jarida a Kano ta bayyana yadda sahar Facebook ta taimaka mata ta samu mijin aure na sunnah
- Soyayyar Zainab da Hussaini ta kullu ne bayan kusan shekara guda, daga watan Agusta zuwa Satumban shekarar 2024
- Ta bayyana yadda nemo taimakon aiki da take wallafawa a shafinta na Facebook ya jawo alakar da ta kai ga aure
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wata baiwar Allah, Zainab Ishaq Muhammad ta bayyana yadda ta yi katari da miji na gari a shafin sada zumunta na Facebook.
Zainab, wacce ke koma kiran kanta Mrs. Koya ta bayyana labarin yadda amfani da shafin ya taimake ta.

Asali: Facebook
A sakon da wallafa a shafinta na Facebook, Zainab ta ce ta ga dacewar ta bayyana haka domin ya zama darasi ga wasu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Facebook: Yadda matashiya ta samu miji a Kano
Hajiya Koya ta bayyana cewa a baya tana yawan wallafa sakonni domin neman aiki ko taimako ga wasu mutane a dandalin sada zumunta, har ta daina daga baya.
Ta ce:
“Da dai ban so na ce komai ba akan haduwar aurenmu da wannan sahar, amma bari in dan baku labari, saboda ya zama darasi."
A cewarta, a ranar 6 ga Mayu, 2023, ta wallafa wani sako na neman aiki da safe, sannan ta ci gaba da harkokinta kamar yadda ta saba.

Asali: Facebook
Bayan kwana biyu ne wani sako ya shigo mata, ashe wannan mutumin da za ta aura bayan ta yi sanadin ya samu aikin yi.
Haduwar Zainab da mijinta a Facebook
Zainab ta ce a lokacin da ta shiga ajen sakon, sai ta ga maganar wanda daga baya ya zama mijinta, inda ya ce ya samu aiki ta hanyar daya daga cikin tallace-tallacenta da ta yi a baya, kuma ya gode mata sosai. Ta amsa masa cikin farin ciki, kuma daga nan ne aka fara mu'amala da juna na tsawon wani lokaci.
A cewarta, bai bayyana cewa yana sonta ba sai bayan kusan shekara guda da haduwarsu, wanda ya zo tsakanin watan Agusta zuwa Satumba, 2024.
Zainab ta bayyana cewa an daura aure a ranar 25 ga Mayu, 2025, kuma ta ce wannan ya nuna cewa har yanzu akwai mutanen kirki a dandalin Facebook.
Legit Hausa ta fahimci an daure wannan auren ne a karamar hukumar Gwale a Kano.
Ta ce:
“Akwai maza da mata na kirki a sahar nan. Don haka duk wanda yake son wata ko wata ke son wani, in kun yadda da amincin sa, kawai ku yi aure."
Ta kammala da gode wa Allah bisa nasarar auren da suka kulla, tare da jaddada cewa za a ci gaba da dacewa.
Barau ya yi ta'aziyyar matasan Kano
A baya, mun wallafa cewa Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan 'yan wasan Kano guda 22 da suka rasu.
A yayin ziyarar, ya mika tallafin Naira miliyan ɗaya ga kowanne daga cikin iyalan mamatan domin rage musu radadin wannan babban rashi da suka yi.
Sanata Barau ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi da ya girgiza Najeriya, tare da addu’ar Allah ya gafarta musu, ya azurta su da Aljannatul Firdausi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng